Wata kotun tarayya a Amurka ta umarci gwamnatin Shugaba Donald Trump da ta gaggauta maido wa kafafen yaɗa labarai na CNN, MS NOW da Politico izinin shiga Fadar White House, bayan an soke takardun izinin shiga da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukan jarida. Alkalin kotun, Timothy Kelly, ne ya bayar da umarnin wucin gadin a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026.
Umarnin kotun ya buƙaci jami’an gwamnatin da abin ya shafa, ban da Shugaba Trump, da su “gaggauta mayar da izinin shiga” ga ma’aikatan kafafen uku. Matakin na wucin gadi zai ci gaba da aiki na tsawon kwanaki 14, sai dai idan kotun ta sake bayar da wani umarni.
Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da CNN, da MS da NOW da Politico suka shigar a ranar 21 ga Satumba, bayan gwamnatin Trump ta soke izinin shigarsu Fadar White House a ranar 18 ga Satumba. Kafafen sun bayyana cewa matakin ya take haƙƙinsu na ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yancin aikin jarida da Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya tanada.
Trump ya sanar da hana kafafen shiga ne bisa zargin cewa suna yaɗa labaran ƙarya game da shi da gwamnatinsa. Sai dai kafafen sun kalubalanci matakin a kotu, suna mai cewa bai kamata gwamnati ta hana ’yan jarida shiga Fadar White House saboda irin rahotannin da suke wallafawa ba.
Alkalin ya bayar da wannan umarni ne yayin da shari’ar ke ci gaba da gudana. Matakin ya tilasta wa gwamnatin Trump maido da damar aikin jarida ga kafafen uku aƙalla na tsawon kwanaki 14, yayin da ake jiran matakan shari’a na gaba.













