Clement Isong, Sakataren zartarwa na kungiyar ‘yan kasuwa sayar da man fetur na kasa wato MEMAN, ya sanar da cewa, kungiyar za ta gudanar da tattauna wa da matatar man fetur ta Dangote.
A cewarsa, kungiyar za ta yi tattanwar ce, musamman domin fahimtar shirin matatar ta Dangote, na samar da mai kai tsaye ga gidajen mai a fadin Nijeriya.
- Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
- Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
Sakataren ya sanar da haka ne haka a wani taron da ta gudanar ta kafar yanar gizo.
Ya ci gaba da cewa, yan kasuwar za su kuma yi hulda da hukumar kula da hakowa da kuma tace man ciki har ma sauran masu ruwa da tsaki, da ke a fannin.
Sakataren ya sanar da cewa, a yanayin da ake ciki a yanzu, kungiyar na kallon kasuwar yadda take gudana.
Ya bayyana cewa, kungiyar na ci gaba da nazartar na rabar da man kai tsare, na shirin na matatar man ta Dangote, wanda daga baya, kungiyar za ta shiga cikin shirin gadan-gadan.
Clement, ya sanar da cewa, kafin kungiyar ta shiga cikin shirin kai tsaye, yana da kyau a fara tattaunawa da Dangoten da kuma sauran da hukumomi.
A cewarsa, ta hanyar tattaunawar ce, za ta sanya kungiyar ta shiga cikin shirin, domin a yanzu, muna ci gaba da yin nazari ne, kan shirin na Matatar ta Dangote.
Sakataren ya ci gaba da cewa shirin da matar ta Dangote ta bullo dashi na rabar da man kai tsaye, musamman iskar Gas, abu ne da kungiyar take gani ya dace.
“Shirin CNG manufa ce ta gwamnati. Yana da manufofin da har yanzu ake aiwatarwa.
Ba mu da isassun kayayyakin more rayuwa na CNG. Don haka, dole ne a yi shiri mai kyau don samun damar aiwatar da shi. Kamfanoni masu ƙarfi ne da za su yi amfani da damar da ake da su,” inji shi.
A makon da ya wuce ne dai, matatar ta Dangote ta ayyana fara wanzar da wannan shirin nata, na rabar da man kai tsaye, zuwa ga gidajen sayar da man fetur da ke a daukacin fadin kasar.
Shirin dai, zai fara ne, a ranar 15 na watan Agustan shekarar 2025, wanda za fara da jigilar man a cikin motocin mai guda 4,000.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp