Kwanaki 100 na farkon Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, sun cika tare da yabo da kuma suka daga mabambantan bangarorin al’ummar wannan kasa.
A kwanaki 100 kacal na jaririyar gwamnatin, ta kara jefa al’ummar kasar cikin kangin fatara da talauci fiye da wanda suke ciki a gwamnatin Buhari da ta gabata, ta yadda mafi yawan jama’a ke kokawa tare da korafin cewa, sun yi zaben tumun dare dangane da gwamnatin da suka ce alkiblar da ta dosa ba mai bullewa ba ce.
- Yadda Tinubu Ya Yi Nasara Kan Abokan Hamayyarsa Atiku Da Obi
- Juyin Mulki: Shugaban Kasar Gabon Ya Shaki Iskar ‘Yanci Bayan Hambarar Da Gwamnatinsa
A yayin da ya karbi mulki a matsayin mutum mafi daraja ta daya a Nijeriya; a 29 ga Mayu, Shugaba Tinubu ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin wannan kasa, wanda ya yi bahaguwar tabarbarewa a baya, lamarin da wasu ke yabawa gabanin fara gani a zahiri.
Tinubu dai na ci gaba da bai wa ‘Yan Nijeriy hakuri kan matsin da suke ciki yana mai tabbatar musu da cewa ‘bayan duhu sai haske’. Amma yaushe? wannan ita ce tambayar da galibin ‘yan kasar ke yi.
Tattalin Arziki
Masana da dama kan tattalin arziki na ganin shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki da gwamnatin ta bullo da su suna da zaki da kuma daci a lokaci guda.
Bayanai sun nuna, sakamakon karyewar darajar naira da cire tallafin mai da aka yi sun haifar da hauhawar farashi da kashi 24.08 a watan Yulin wannan shekara. A ranar 14 ga watan Yuni, Babban Bankin Nijeriya ya umarci bankuna da su sayar da kudaden waje ba tare da wani tarnaki ba a kan farashin kasuwa. Wannan dalili ne yasa farashin naira ya yi tashin gwauron zabo, zuwa naira 915 a kan kowace dala 1 a kasuwar bayan fage.
Da yake tattaunawa da Jaridar Daily Post a makon jiya, fitaccen masani tattalin arziki, Tsohon Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Banki, Farfesa Segun Ajibola ya bayyana cewa, an dauki matakai kwarara a watanni uku na Tinubu wadanda tsawon shekaru ake ta tsoron dauka.
“Daura damarar yaki da cin hanci da kawar da gurbatattun abubuwa a fannoni mafi tasiri na tattalin arziki a cikin kwanaki 60, ba karamin babban abin yabawa ba ne,” kamar yadda ya bayyana.
Ya ce, aikin da Shugaban Kasa ke yi tare da hadimansa da Ministoci da sauran makamantansu, hannaye ne da za a ga alfanunsu, domin a yanzu haka a kan ga kyakkyawar makomar tattalin arziki ta hanyar nada kwararru tare da ci gaba da daukar gogaggun ma’aikata, wadanda suka yi fice a cikin gwamnatinsa; domin sauke nauyi.
Sai ya ce, amma wajibi ne ‘yan Nijeriya su yi la’akari da farfadowa tare da dawowa da martabar gurbataccen tattalin arzikin Nijeriya, ba zai yiwu a dare daya ba. A cewar tasa, babban kalubalen shi ne fahimta da hadin kan dukkanin al’umma, domin a cewarsa yana da tabbacin gwamnati za ta dauki matakin da ya dace na samun nasara.
Shi ma a nasa bangaren, Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin ‘SD & D Capital Management’, Idakolo Gbolade cewa ya yi, watanni uku na farko na Tinubu sun zo wa talakawa da tsauri, sai dai ya ce shirye-shiryen da aka fito da su sun samar da sabuwar rayuwa ga tattalin arziki bayan gwamnatin ta karbi mulki a mummunan yanayin rugujewar tattalin arziki.
“Kwakkwaran matakin cire tallafin man fetur da kuma kokarin daga martabar naira, duka an yi ne domin bunkasa tattalin arziki. Dakatarwa tare da binciken dakataccen Gwamnan Babban Bankin Kasa kuma, abu ne da aka yi tsammani a bisa ga illar abubuwan da ya aiwatar ga jama’a da tattalin arzikin kasa.”
Ya ce, abin da ya kamata gwamnati ta yi a gajeren zango shi ne, yin hanzarin samar da tallafin rage radadin cire tallafin mai ga al’umma tare da aiwatar da shirye-shiryen bunkasa aikin gona, tallafawa kamfanoni da sauran kananan masana’antu ta hanyar ba su bashi, domin bunkasa tattalin arziki.
A dogon zango kuwa ya ce, a zuba jari a fannin man fetur da gas, ma’adinai, makamashi da kuma aikin gona tare da kulawa ta musamman ga kananan masana’antu, domin bunkasa su. Haka zalika ya kara da cewa, gwamnatin ta dauki matakin samar da hanyar daina amfani da man fetur a zirga-zirga ta hanyar juyawa daga fetur zuwa gas, domin saukaka wa al’umma tare da baiwa matasa ayyukan yi, sai kuma daga karshe ya ce gwamnatin ta guji tsarin ciwo bashi irin na gwamnatin da ta gabata, wadda ta kai Nijeriya ga halin da take ciki yanzu.
Cire Tallafin Mai
Cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi a jawabinsa na karbar mulki, shi ne babban abin da ya dauki hankalin jama’a tare da girgiza su, musamman bisa ga radadi da kuncin da matakin ya jefa kasa da ‘yan kasa a cikibaki-daya.
Garan Bawul A Musayar Kudade
Babban Bankin Nijeriya, ya bayar da sanarwar fitowa da sabbin ka’idoji na hada-hadar kudade, domin farfadowa da daga darajar naira. Daga cikin dokokin, akwai kafa sabuwar kasuwa ta musamman, wadda za ta rage bukatar amfani da kudaden waje.
Karin Farashin Fetur
Karin farashin man fetur da gwamnati ta yi sakamokn cire tallafin man fetur, ya kara sanya al’umma a cikin kunci da fatar. Kazalika, al’ummar kasa sun fito fili sun yi Allah- wadai da karin, kamar yadda kungiyoyin kwadago suka bukaci gwamnati ta tausayawa jama’a ta rage farashin.
Farashin man fetur din, ya tashi daga naira 195 zuwa 537 bayan cire tallafin man, sai kuma karin farashi na biyu da man ya yi zuwa 615 zuwa 650, lamarin da ya kara gurbata al’amura, rayuwa ta kara yin tsada.
Nada Shugabannin Tsaro
A ranar 19 ga watan Yuni, Shugaba Tinubu ya kori Shugabannin Hukumomi Tsaro tare da maye gurbinsu da sababbin jami’an da za su jagoranci tabbatar da tsaron kasa.
Shugabannin da suka hada da Hafsan Hafsoshi da kuma Shugaban Rundunar Sojin Kasa, Sojin Sama da Sojin Ruwa, Shugaba Tinubu ya dora musu alhakin kakkabe ayyukan ta’addanci a fadin wannan kasa baki-daya.
Dakatar Da Emefiele Tare Da Bincikensa
A ranar 9 ga watan Yuni, Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Kasa, Godwin Emefiele. Sanarwar dakatar da shi din ta bayyana cewa, an dauki matakin ne domin gudanar da bincike tare da sauya fasalin harkokin kudade da ya jagoranta a Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Tinubun ya dauki matakin dakatar da Gwamnan Babban Bankin Kasar, wanda tsohon Shugaba Jonathan ya nada a 2014, makwanni biyu bayan karbar mulki. Tuni dai jami’an tsaron farin kaya, suka gabatar da shi a gaban kotu da tarin tuhume- tuhume 20 a shari’ar da ake ci gaba da gudanarwa, bayan janye tuhumar farko ta mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Dakatar Da Shugaban EFCC
Shugaba Tinubu ya dakatar da Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC, Abdurrashid Bawa a ranar 14 ga Yuni, wanda har zuwa yau yake ci gaba da zama tsare a hannun jami’an tsaron DSS, ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan laifukan da ake tuhumarsa da su ba. Tuni dai Bawa ya garzaya kotu yana kalubalantar tsare shin ba bisa ka’ida ba.
Dokar Baiwa Dalibai Bashi
A matakai na farko-farko da Gwamnatin Tarayya ta dauka karkashin jagorancin Shugaba Tinubu shi ne, sanya hannu ga dokar baiwa daliban kasar bashi. Dokar bashin wadda ita ce irin ta ta farko a Nijeriya, bayar da rancen ya shafi daliban manyan makaratu da suka fito daga gidaje masu karamin karfi, domin su samu damar rancen karatu maras ruwa daga gidauniyar bayar da bashin karatu ta kasa.
Rushe Shugabannin Hukumomi
A wata na biyu na mulkinsa, Shugaba Tinubu ya rushe dukkanin Shugabannin Hukumomin Gwamnatin Tarayya. Hukumar Zabe ta Kasa da wasu Hukumomi 13, sun tsallake shiga cikin hukumomin da aka rushe. Tuni aka fara aikin zakulo wadanda za su maye gurbinsu.
Nada Ministoci
A kasa da kwanaki 60 na mulkinsa, Shugaba Tinubu ya tura sunayen Ministoci ga Majalisar Dattawa, domin tantance su. A kashi na farko, shugaban ya aika da sunaye 28, daga baya kuma ya sake aikawa da kashi na biyu mai dauke da sunaye 19, wadanda suka zama ‘Yan Majalisar Zartaswar Gwamnatin Tarayya 47.
Rikita- Rikitar Nijar
A sakamokn juyin mulkin da sojoji suka yi na hambarar da gwamnatin farar hula a Jamhuriyar Nijar, lamarin ya shafi Nijeriya kai tsaye. Shugaba Tinubu, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Kasashen ECOWAS, ya jagoranci taron kungiyar a inda aka cimma matsayar afkawa Nijar da yaki idan ba su mayar da mulki ga Gwamnatin Dimokuradiyya ba. Tuni dai rikita-rikitar ta Nijar ta durkusar da al’amura da dama a Nijeriya tare da zama silar karin farashin abubuwa da dama, musamman ta fuskar shigowa da abinci da sauran kayan bukatu, wanda a yanzu kuma dubban motoci ne ke tsaye dauke da kaya babu damar shiga ko fita.
Hauhawar Farashi
Ya zuwa yanzu, al’umma na cike da kunci sakamakon hauhawar farashin dukkanin abubuwan da rai ke bukata, ta yadda abubuwa da dama musamman abinci ke kokarin buwayar talaka.
Jadawalin hauhawar farashi na wannan shekara, ya karu zuwa kashi 24.08 a Yuli daga kashi 22.79 a Yuni kamar yadda ofishin kididdiga na kasa ya bayyana a tsakiyar watan Agusta. Rahoton ya nuna hauhawar farashin abincin ya tashi zuwa kashi 26.98 a Yuli daga kashi 25.25 a Yuni.
Duk da cewa, farashin abinci yana tashi sama a fadin kasa tsawon shekaru, amma yanayin a wannan lokacin ya ta’azzara ne sosai sakamakon illar shirye-shiryen gwamnati, musamman na cire tallafin man fetur da sauran makamantansu. Hukumar ta bayyana cewa, hauhawar farashin abincin shakara zuwa shekara yana faruwa ne bisa dalilin tashin farashin man fetur da sauransu.
Karuwar Talauci
Al’ummar Nijeriya da ke fama da talauci a zamanin gwamnatin da ta gabata, sun kara talaucewa kwarai da gaske a cikin kwanaki 100 na mulkin Tinubu.
Kungiyar ‘World Poberty Clock’ ta bayyana cewa akwai mutane miliyan 71 da ke fama da talauci a Nijeriya kamar yadda sakamakon kiddigar bincikensu na 2023 ya bayyana. ‘World Poberty Clock’, madubi ne da ake auna talauci a duniya. A cewar tasu mutane miliyan 133 ne matsakaitan matalauta a Nijeriya.
Tsananin talaucin da al’umma ke fama da shi a yanzu, ya sa mafi yawan jama’a kasancewa cikin kuka da kokawa da yadda mulkin Tinubu ya zo musu, wanda a baya suke fatan samun saukin al’amura bayan karewar Gwamnatin da ta gabata, amma sai ga shi talaucin da ake fama da shi a halin yanzu ya fi na baya tsanani.
Matsalar Musayar Kudade
Gagarumar matsalar harkokin musayar kudade, babban tarnaki ne ga bunkasa tattalin arzikin wannan kasa. Wasu tsare-tsare da Babban Bankin Kasa ya fito da su kan musayar kudade tare da dawowa da cibiyoyin musayar kudaden bayan dakatar da ayyukansu da gwamnatin da ta gabata ta yi, ya kara haifar da illa ga tattalin arziki ta yadda darajar naira ke ci gaba da faduwa.