• English
  • Business News
Sunday, May 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwana 6 Ga Rantsar Da Tinubu: ‘Yan Jarida Sun Yi Tsokaci Kan Yadda Aka Miƙa Mulki A Gwamnatocin Baya

by Sadiq
2 years ago
in Manyan Labarai
0
Kwana 6 Ga Rantsar Da Tinubu: ‘Yan Jarida Sun Yi Tsokaci Kan Yadda Aka Miƙa Mulki A Gwamnatocin Baya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin da ya rage kwanaki shida kacal da rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya, a jiya jiga-jigan ‘yan jaridun fadar gwamnatin kasar nan sun yi waiwaye kan yadda ake tafiyar da harkokin mika mulki.

Daga cikin abubuwan da suke faruwa a wajen bikin, ciki har da halartar manyan baki wajen bikin, da kuma jawabai na tunawa da sabon shugaban da aka rantsar, ’yan jarida, wadanda aka fi sani da wakilan gidan gwamnati, sun zanta da LEADERSHIP kan abubuwan da za su kayatar a wajen bikin rantsuwar.

  • Sarkin Kano Ya Bukaci Tinubu Ya Kafa Ma’aikatar Harkokin Addinai
  • Buhari Zai Kaddamar Da Ayyuka 7 A Ranar Talata –Fadar Shugaban Kasa

Wata babbar ‘yar jarida mai suna Chesa Chesa, wadda ke daukar rahoto a fadar gwamnati tun a shekarar 2008, ta ce yanayin da ake ciki a lokacin mika mulki ana sa ran faruwar abubuwa da dama.

A cewarsa, an mai da hankali sosai kan jawabin shugaban kasa mai jiran gado, inda da yawa ke jiran su ji sanarwa ko yanke shawara da za su nuna alkiblar sabuwar gwamnati.

Ta ce jama’a, wadanda aka gayyata da wadanda ba a gayyace su ba, sun yi cincirindo a dandalin Eagle Square, wanda ‘yan sanda suka yi wa tsinke. Yanayin yawanci kamar biki ne. Har ma a wajen dandalin Eagle Square inda ake rera wakoki ga sunan sabon shugaban kasa da jam’iyyarsa ta hayar kida.

Labarai Masu Nasaba

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci

“Ana kewaye filin rantsar da shugaban kasa da jami’an tsaro. Sannan mutane kan yi kasuwanci daga nesa da harabar filin.

“Akan mai da hankali sosai kan shugaban kasa, kuma ba a kan mataimakin shugaban kasa ba. A ko da yaushe akwai shugabannin da ke kawo ziyara, musamman shugabannin Afirka. Yana daya daga cikin lokutan da sojoji da jami’an tsaro ke yin, fareti.

“Yawanci a kan yi raye-raye masu ban sha’awa da wasan kwaikwayo, wadanda ke nuna manyan kabilun kasa. Tabbas, baki, musamman masu manya-manya kan halarci taron cikin shiga ta alfarma.

“Abin sha’awa shi ne, za a ga shugaba mai barin gado tare da rakiyar matarsa. Bayan rantsar da sabon shugaban da mataimakinsa, shugaban da mataimakinsa mai barin gado sukan bar sashen manyan baki. Dukka bikin yana daukar kimanin sa’o’i uku ne ko fiye da haka,” in ji Chesa.

Wani babban da jarida, Sunday Ode, wanda bai wuce shekaru 13 ba a matsayin wakilin gidan gwamnati ya tafka muhawara a kan kudirin shugaban kasa, ya tuno jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, inda ya ce shi na kowa ne, sannan ba kowa ba.

Ode wanda ya yi tsokaci kan bikin rantsar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo karo na biyu, da kuma bikin rantsar da Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, Goodluck Jonathan da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce, “Kamar ‘yan siyasa, yawanci yana daya daga cikin abubuwan da ‘yan jarida ke sa rai tare da kyakkyawan fata dangane da batun fayyace bayanai da kuma alkawuran da kowane sabon shugaban kasa zai yi.

“Kar ku manta Yar’Adua ya girgiza duniya lokacin da ya bayyana cewa zaben da ya haifar da shi bai inganta ba. Kuma kar ku manta Buhari ya ce “Ni na kowa ne, ba na kowa ba ne”.

“Faretin sojoji yawanci abin kallo ne a duk taron kaddamar da ko dai wadanda ke kasa a dandalin Eagle Square ko kuma wadanda ke kallo daga nesa”.

Ode ya ci gaba da cewa, babban lokacin da ake gudanar da duk wani nadin sarauta, musamman ma wanda ya kawo sabuwar gwamnati, shi ne lokacin da shugaban kasa mai barin gado ya sauka daga mukaminsa kamar yadda aka yi tsakanin Jonathan da Buhari.

Bikin rantsar da Tinubu zai kayatar –Agbakoba

A halin da ake ciki kuma, babban mai fafutukar kare hakkin bil’adama, kuma kwararre a fannin shari’a, Cif Olisa Agbakoba (SAN), a jiya ya ce rashin tabbas da aka samu a bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai sa taron ya zama abin tunawa.

Agbakoba, babban jigo a fafutukar tabbatar da dimokuradiyyar kasa, ya jaddada cewa kararrakin da ake jira ba zai iya dakatar da kaddamar da shirin mika mulki ba, inda ya kara da cewa ba zai iya tunawa akwai wani lokaci da aka gabatar da irin wadannan koke-koke na dakatar da bikin rantsuwa ba.

Ya ce, “Batun da ya fi muhimmanci kamar yadda nake gani, shi ne damuwar ko za a yi bikin rantsuwa. Ina ganin wannan shi ne batun da ya fi daukar hankali wanda zai sa bikin ya zama abin ban mamaki fiye da sauran.

“A gare ni da kaina, ta fuskar doka, wannan bikin ba za a iya hana shi gudana ba saboda abin da ya faru, cewa an shigar da kara a kotu don haka dole ne mu jira.

“Abin mamaki game da ni a ce an hana yin rantsuwa. Wannan shi ne abin mamaki a gare ni.

Ya Kamata A Rantsar Da Zababbun Ma’aikata – Sanata Okurounmu

Shi ma da yake nasa jawabin, Sanata Femi Okurounmu ya ce bai kamata a ce rantsar da zababbun masu mukamai ya samu tasgaro ba.

Sai dai ya ce abin da ake sa rai daga shugaban kasa mai jiran gado shi ne zai magance matsalolin da ke addabar Nijeriya.

Ya ce, “Ba matsalolin da ‘yan Nijeriya ke son a magance su kadai ba, a’a, wasu matsalolin da shi da kansa ya yi a lokacin da yake karkashin Cif Obafemi Awolowo da Abraham Adesanya ya kwashe tsawon wadannan shekaru kafin ya koma APC. Ina fata har yanzu zai tuna da wadannan abubuwan kuma ya kula da su.

‘’Sauran abin da ake sa rai shi ne ya koma tsarin mulkin 1953. Wannan yana daya daga cikin fifikon farko. Kundin tsarin mulkin da muke aiki da shi a yanzu yaudara ne, almubazzaranci ne, yana da tsada, mulkin kama karya ne, ba dimokradiyya ba.

“Idan ya koma ga kundin tsarin mulki na 1953, tare da gyare-gyaren da ya kamata, abin da nake ji shi ne, mu koma ga Jihohi 12 na Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) da aka kirkira lokacin yana shugaban kasa na soja.”

A kan yadda hakan zai iya kasancewa, Okurounmu ya ce, ”Na ce ya koma wancan tsarin. Idan ya yarda ya koma tsarin, me ya sa hakan bai tabbata ba? Mun gudanar da jihohi 12 a karkashin Gowon; za mu iya komawa tsarin. Kuma mun gudanar da kundin tsarin mulki na 1953- shi ne abin da muka yi aiki daga 1960 zuwa 1966 kuma ya yi mana amfani sosai.

Hukumomin Tsaro Sun Fara Sa Ido Sosai A Eagle Square

Gabanin bikin rantsar da sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, hukumomin tsaro sun fara atisaye sosai a dandalin Eagle Square.

Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa jami’an rundunar Sojin Nijeriya (AFN) da na ‘yan sandan Nijeriya da sauran jami’an tsaro masu alaka da su sun fara atisayen da rangadin tunkarar ranar 29 ga watan Mayu.

Wakilanmu sun tattaro cewa sojojin da aka tura domin fareti sun kwashe sama da mako guda suna atisaye.

An kuma bayyana cewa, wannan shi ne tsarin shirye-shiryen da ake yi gabanin bukukuwan rantsuwa a shekarar 2019.

Duk da cewa wurin zai cika makil da sojoji, ba a rufe hanya ba.

Sai dai a cikin wata takarda da LEADERSHIP ta gani, majalisar rikon kwarya ta shugaban kasa ta umarci hukumomin tsaro da su killace dukkan yankunan da ke kusa da dandalin Eagle Square daga karfe 2 na rana a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu zuwa Talata 30 ga watan Mayun 2023.

Wani bangare na takardar da Dokta Ngozi Onwudiwe, babbar sakatariya ta ofishin jin dadin ma’aikata ta shugaban ma’aikatan tarayya ta sanya wa hannu ta ce: “Kamar yadda kuka sani, Majalisar mika mulki ta Shugaban kasa (PTC) ta kaddamar da ayyuka na bikin rantsar da shugaban kasa. Faretin rantsar da zababben shugaban kasaSanata Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne kololuwar shirin da zai gudana ne a ranar Litinin 29 ga Mayu, 2023 a dandalin Eagle Square.

“A bisa tsarin tsaro na taron, Jami’an tsaro za su killace harabar sakatariyar gwamnatin tarayya ta l, Il, IIl da kuma ma’aikatar harkokin waje daga karfe 2:00 na rana ranar Juma’a, 26 ga Mayu, 2023 zuwa Litinin, 29 ga Mayu 2023. Saboda haka, jami’ai da masu ziyara a yankunan da abin ya shafa ba za su bi hanyar ba har zuwa Talata, 30 ga watan Mayu, 2023.”

A halin da ake ciki kuma, rundunar soji a karo na goma sha uku, ta ce babu wata barazana ga mika mulki a ranar 29 ga watan May.

Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja ya ce, “Kamar yadda na fada muku akwai kwamitin mika mulki da aka kafa kuma mambobin kwamitin mika mulki da suka hada da jami’an soji da sauran jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana domin ganin komai ya yi nasara”.

Haka kuma, Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba, ya ce bikin ranar 29 ga watan Mayu zai samu tsaron da ya dace.

Ya kuma bayyana cewa, aikin da tsarin mulkin kasar nan ya bai wa rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta hada tare da tabbatar da tsaron tsare-tsaren da za su kai ga kaddamar da zababbun ‘yan takara a dukkan matakai da bayar da tabbacin gudanar da bukukuwan nadin cikin nasara.

Don haka, ya ce, “Za mu gudanar da wannan aiki da kyau kuma a bayyane. Duk wanda ya tsaya kan hanya za a kamo shi sannan ya dandana kudarsa.

“Saboda haka, an karfafi ‘yan kasa da su kasance masu lura da abubuwan da suka shafi siyasa wadanda za su so su yi amfani da sha’awarsu ta siyasa don ci gaba da kada su manufofin da ba su dace ba, rashin dimokuradiyya, da kuma rashin bin tsarin mulki.

“Ya kamata su bijirewa irin wannan, su gudanar da sana’o’insu na halal, sannan su zama masu kishin kansu.

“An kuma kara musu kwarin gwiwa da su gaggauta kai rahoton duk wani yunkuri na bata-gari na siyasa na kutsa kai wajen taro don tada tarzoma.

“Haka zalika, an gargadi ‘yan siyasa marasa kishin kasa wadanda za su iya haifar da tashin tashina musamman a kafafen sada zumunta da su kiyaye kalamansu. Dimokuradiyyarmu za ta ci gaba da tafiya yadda ya kamata, don tsarin tsaron kasar nan ya tabbata, kuma za a gudanar da bikin rantsar da shugaban kasa kamar yadda aka tsara a cikin kwanciyar hankali.”


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yan JaridaMika MulkiRantsuwaSharhiTinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sarkin Kano Ya Bukaci Tinubu Ya Kafa Ma’aikatar Harkokin Addinai

Next Post

An Kwashe Wa Juventus Maki 10 A Gasar Seria A

Related

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar
Manyan Labarai

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

1 hour ago
Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci

23 hours ago
Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya
Manyan Labarai

Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya

1 day ago
Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje
Manyan Labarai

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

2 days ago
Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai
Manyan Labarai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

2 days ago
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa
Manyan Labarai

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

3 days ago
Next Post
An Kwashe Wa Juventus Maki 10 A Gasar Seria A

An Kwashe Wa Juventus Maki 10 A Gasar Seria A

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu

May 11, 2025
Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

May 11, 2025
Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

May 11, 2025
Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

May 11, 2025
Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

May 11, 2025
Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

May 11, 2025
Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari

Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari

May 11, 2025
Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

May 10, 2025
An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

May 10, 2025
Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

May 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.