Ƙungiyar Kwankwasiyya ta shirya gudanar da bukukuwa na musamman domin murnar cikar jagoranta, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shekaru 70 a duniya, a Kano.
Bisa sanarwar da Yusuf Kofarmata ya fitar, za a fara bukukuwan a ranar Laraba, 21 ga Oktoba, 2026, da baje kolin ilimi da ƙarfe 10:00 na safe a gidan Kwankwasiyya, da ke Miller Road, Kano.
Haka kuma, za a gudanar da taron tattaunawa mai taken RMK’s Birthday Platinum Jubilee Colloquium da ƙarfe 3:00 na rana a The Afficent Grand Marquee, Magaji Rumfa, Kano.
ADVERTISEMENT
A ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, kuma an tsara ziyartar asibitoci, gidan marayu da wuraren da rikice-rikice suka raba mutane da muhallansu.














