Yau ranar 19 ga watan Oktoba, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da bayanai da suka nuna cewa, a watanni tara na farkon bana, tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba, inda ya ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba. Bisa kididdiga ta mataki na farko, jimillar kudin da aka samu wato GDPn kasar ya karu da kashi 4.6% idan an kwatanta da makamancin lokacin a shekarar da ta gabata.
A hakikai dai, tattalin arzikin kasar a watanni tara na farkon bana, ya ci gaba da tafiya cikin matsin lamba, yana mai bayyana alamar ci gaba bisa karfin kirkire-kirkire da ingantaccen tsari. Ban da wannan kuma, ana samun ci gaba cikin sauri wajen samar da kayayyaki, yayin da cinikayyar waje ta samu kyakkyawan ci gaba, kana guraben aikin yi da farashin kayayyaki sun kasance cikin kyakkywan yanayi gaba daya, kuma ana tabbatar da ganin jama’a sun samu ingantacciyar rayuwa, kuma juriya da kuzarin ci gaban tattalin arziki na kara bayyanawa.
Sai dai a wani bangare daban, ya kamata a lura cewa yanayin kasa da kasa yana da sarkakiya, kuma yana canzawa, matsalar karancin bukatu a cikin gida ma har yanzu tana bayyana sosai, kuma ana bukatar karfafa ingancin tushen tattalin arzikin dake tafiya cikin kwanciyar hankali. A mataki na gaba kuma, dole ne a ci gaba da bin jagorancin shugaban kasar Xi Jinping na gina tsarin gurguzu mai sigar musamman ta Sin na sabon zamani, don nace ga bin ka’idar ci gaba cikin kwanciyar hankali, da aiwatar da sabon ra’ayin samun ci gaba yadda ya kamata a duk fannoni, da kuma hanzarta gina sabon tsarin ci gaba. Kazalika da ci gaba da zurfafa gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga ketare, da karfafa karfin jagoranci na kirkire-kirkire da mai da hankali kan amfani da karfin manufofin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare. Haka kuma da kara karfin fadada bukatun cikin gida da inganta karfin samar da kayayyaki, kana da tabbatar da inganta rayuwar jama’a, ta yadda za a ingiza samun bunkasar tattalin arziki mai inganci.
Bugu da kari, a bana jimillar hatsin lokacin zafi wato yawan shinkafar da aka girbi yanzu ya kai ton miliyan 179.04, wadda ta karu da ton dubu 780 idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, wato ya karu da kashi 0.4%. Ban da wannan kuma, noman hatsin kaka yana tafiya cikin yanayi mai kyau, kuma ana sa ran a duk shekara, za a sake samun nasarar girbi mai armashi. (Amina Xu)














