Yau kimanin shekaru tamanin ke nan da samun gagarumar nasarar Sin a kan yakinta da maharan kasar Japan da kuma yaki kan mummunar akidar nan ta mulkin danniya, wato fascism a Turance, a fadin duniya. Yunkurin na Japan na afkawa Sin ya faro ne tun shekarar 1931, yayin da maharan na Japan suka afkawa yankin Manchuria, suka fara aiwatar da kisan kare dangi kan fararen hula ba gaira ba dalili. Daga bisani a watan Disamban shekarar 1937, suka kutsa kai a birnin Nanjing, wato babban birnin kasar Sin a wancan lokaci, inda maharan suka hallaka fararen hula da fursunonin yaki sama da dubu 300.
A bana ce dai kasar ta Sin take bikin cika shekaru 80 da samun nasara a kan maharan Japan da kuma yakin duniya kan akidar nan ta mulkin danniya.
Shekaru 14 ne sojojin na Sin suka kwashe suna gumurzu da maharan na Japan, inda daga bisani suka samu galaba a kan maharan na Japan.
Wannan dai shi ne yaki mafi dadewa kuma mafi tsada a tarihin kasar Sin da sojoji suka aiwatar domin ‘yanto da ‘yan kasa.
Mutane masu hangen nesa da sanin ya kamata ne daga Sin da sauran kasashen duniya suka matsa kaimi da sadaukar da kai ba tare da sanyi a gwiwa ba, suka hada karfi da karfe wajen kawo karshen mummunar akidar nan ta mulkin danniya, abin da ya kawo sauyi mai ma’ana a tarihin karni na 20, tare da bude wani sabon babi na yin watsi da akidar yaki tare da rungumar akidar zaman lafiya.
Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar rayukan da za su kai sama da miliyan 100, wadanda daga cikinsu sojoji da fararen hula miliyan 35 ne Sin ta yi asara.
Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan mummunar akida ta mulkin danniya, yayin da ta shiga cikin sahun sojojin sauran kasashe a yakin duniya na biyu. Kafada da kafada suka yi gumurzu wajen murkushe maharan kasashen Japan, Jamus da Italiya.
A wannan gabar, za mu fahimci cewa, samun nasarar da Sin ta yi a kan maharan na Japan da kalubalantar akidar mulkin danniya ya amfanawa sauran kasashen da suke da tunani iri daya da Sin na samar da kyakyawar makoma ga al’umma.
A yau an wayi gari ana samun sauye-sauye cikin hanzari irin wadanda ba a taba gani ba a cikin karni daya. Ana yawan samun barkewar rikici tsakanin yankuna, yayin da kuma kalubaloli a duniya suke ta kara yawaita a kullum. Don haka kamata ya yi a rinka koyon darasi daga tarihi. Ana iya shawo kan irin wadannan matsaloli ta hanyar adalci, daidaito da kuma tsarin yin garambawul a kan manufofin zamantakewa na duniya. (Lawal Mamuda)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp