ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Labarin Yin Yuzhen Da Salkowski: Makomar Huldar Sin Da Amurka Na Dogaro Da Cudunyar Jama’arsu

by Sulaiman
2 weeks ago
Yuzhen

A filin jirgin sama na kasa da kasa na Ejin Horo dake birnin Ordos na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta, a daren ranar Lahadi 23 ga watan nan, Ba’amurka da ya bakunci garin mai suna “Salkowski” (sunansa na ainihi shi ne Ronald Salkowski), da jarumar kasar Sin mai yaki da hamada Yin Yuzhen sun rungume juna da karfi, suna zubar da hawaye don farin ciki.

A shekara ta 1999, malami Ba’amurka da ke koyarwa a Sin wato “Salkowski” ya ji labarin yadda Yin Yuzhen ta yi iyakacin kokari a hamadar Mu Us, don magance hamada da kuma dashen bishiyoyi, kuma ya tara dalar Amurka 5,000 don taimakawa Yin Yuzhen.

Yanzu haka, bishiyoyin da aka dasa da wannan kudi kyauta, sun girma zuwa itatuwa sama da 50,000. A watan Mayu na bana, Yin Yuzhen ta nemi tuntubar “Salkowski” ta hanyar fitar da bidiyo a duk fadin yanar gizo, kuma daga karshe dai ta cimma nasarar samun “Salkowski” wanda yake da zama a Amurka. Wannan abota da ta ratsa tekun Pasifik, ta zama alama mai rai ta musayar zumunci tsakanin al’ummomin Sin da Amurka.

ADVERTISEMENT

Jama’ar Sin da Amurka su ne tushen dangantakar kasashen biyu. Saduwar Yin Yuzhen da “Salkowski” bayan sama da shekaru 20 ta kara dumama dangantakar Sin da Amurka. Abin da ya shaida cewa, musayar al’adu da tuntubar al’umma su ne tushen dangantakar Sin da Amurka. Abota da hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka suke faranta ran jama’a. Wani binciken ra’ayin jama’a, da cibiyar bincike ta Pew ta Amurka ta fitar a watan Afrilu na bana, ya nuna cewa, adadin jama’ar Amurka dake ganin Sin da kyau ya “kusan ninkawa” a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Rahoton da cibiyar harkokin duniya ta Chicago ta fitar a watan Agusta, ya nuna cewa kashi 59% na Z-generation (mutanen da aka haife su daga shekarar 1995 zuwa ta 2009), da kashi 58% na millennials (mutanen da aka haife su daga shekarar 1981 zuwa ta 1996) sun yarda da tuntuba tare da Sin.Al’ummar Sin da Amurka ne suka ciyar da abotar bangarorin biyu gaba.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

A ranar 24 ga watan, “Salkowski” da Yin Yuzhen sun dawo hamadar Mu Us tare, inda suka dasa dauwwamanmun bishiyoyi 3 da ke wakiltar abota. Abin da suka dasa ba bishiyoyi ce kawai ba, a’a, abota ce da ta wuce iyakokin kasa da zamani. (Amina Xu)

Yuzhen
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026

Next Post
Yuzhen

Mauludi: Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu'o'in Nasara Kan Matsalar Tsaro

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.