A yau Lahadi, ma’aikatar tsaron kasar Sin ta fitar da wani bidiyo, mai taken “Wane ne ke jirkita gaskiyar tarihi?”, wanda a cikinsa ta zargi shirin talabijin kan yakin leken asiri da kasar Japan ta nuna mai suna “VIVANT”, wanda ke kunshe da jirkita gaskiyar tarihi, tare da mayarwa Sinawa laifin azabtarwar da mayaka Japanawa, da sojojin Japan suka aikata kan al’ummar kasar Sin, a wani yunkuri na kawar da laifukan hare-haren da Japan ta aikata a tarihi.
Bidiyon ya jaddada cewa, ba za a iya sauya shaidar tarihi ba, kuma ba za a iya gurbata gaskiya ba.(Safiyah Ma)
ADVERTISEMENT














