Jam’iyyar ADC ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari jihar Sakkwato ta faɗa cikin rikicin siyasa ba, bayan wani harin bindiga da aka kai wa ayarin motocin ɗan takararta na gwamna, Manir Muhammad Dan’iya, a kusa da Filin Jirgin Sama na Sultan Abubakar III. Jam’iyyar ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira ƙaruwar barazanar tsoratar da ƴan adawa gabanin zaɓen 2027.
Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Gwamnan ADC a Sakkwato, Hon. Muhammad Bello Goronyo, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai. Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, jim kaɗan bayan Dan’iya, wanda aka fi sani da Walin Sakkwato, ya raka tsohon gwamnan jihar kuma Sanatan Sakkwato ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, zuwa filin jirgin sama domin komawarsa Abuja. Jam’iyyar ta ce an yi harbe-harbe, sannan aka lalata wasu motocin da ke cikin ayarin.
ADC ta zargi jami’an rundunar Sokoto Marshal ta Jihar Sakkwato da hannu a lamarin, tare da iƙirarin cewa an tsare jami’an DSS guda biyu da ke cikin tawagar tsaron ɗan takarar. Jam’iyyar ta buƙaci ƴansanda, da DSS da Gwamnatin Jihar Sakkwato su gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano waɗanda suka yi harbin da kuma tabbatar da ko akwai wani umarni daga manyan jami’an gwamnati ko na tsaro.
Jam’iyyar ta kuma danganta harin da wasu abubuwan da ta ce sun faru a baya, ciki har da zargin kai wa mata mambobinta hari yayin wani tattakin nuna goyon baya a ranar 28 ga Oktoba, inda ta ce an jikkata wasu mahalarta, an ƙwace wayoyinsu da lalata motoci. Ta kuma yi zargin cewa an kai hari ofishinta na yaƙin neman zaɓe, an lalata babura da kayan kamfen, sannan an lalata allunan tallata jam’iyyar a wasu sassan jihar. Haka kuma, ta yi zargin cewa an matsa wa wasu otel-otel lamba su soke tanadin wuraren da jam’iyyar ta yi domin gudanar da ayyukanta.
ADC ta buƙaci Sufeto-Janar na Ƴansanda da Daraktan DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa su binciki zarge-zargen, su kare ƴan siyasa da magoya bayansu, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi. Ta jaddada cewa jami’an tsaro ya kamata su kasance masu zaman kansu daga siyasa, ba tare da amfani da su wajen takura wa jam’iyyun adawa ba.
Duk da lamarin, jam’iyyar ta ce za ta gudanar da bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, kamar yadda aka tsara. Ta buƙaci magoya bayanta su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da bin hanyoyin shari’a wajen neman adalci.
A nata ɓangaren, rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da samun rahoton harin, amma ba a samu cikakken martani daga Gwamnatin Sakkwato ko hukumomin tsaron da aka zarga kan bayanan da ADC ta gabatar ba.














