ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 1, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba

by Abubakar Sulaiman
3 hours ago

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin neman lamuni mai suna SPARK, wanda zai bai wa ’yan Nijeriya damar samun lamunin kuɗi ta wayar hannu ba tare da buƙatar intanet ko wayar zamani ba.

Kamfanin Nigerian Consumer Credit Corporation (CREDICORP) ne ya ƙaddamar da tsarin, musamman domin taimaka wa mutanen da ba su taɓa karɓar lamuni a hukumance ba ko kuma ba su da tarihin karɓa da biyan bashi. Masu sha’awar amfani da tsarin za su iya danna lambar *347*333# a wayoyinsu domin fara amfani da shi.

A cewar CREDICORP, tsarin SPARK zai sauƙaƙa wa mutane samun lamuni, tare da taimaka musu wajen gina tarihin yadda suke karɓar bashi da kuma biyan sa a kan lokaci. Kamfanin ya ce yin hakan zai iya inganta matsayin masu karɓar lamunin a tsarin hada-hadar kuɗi, tare da buɗe musu ƙarin damar samun tallafin kuɗi a nan gaba.

ADVERTISEMENT

An ƙaddamar da tsarin ne a wajen wani taron CREDICORP mai suna ‘CREDICORP for All’ da aka gudanar a Aba, Jihar Abia. Taron ya haɗa da mazauna yankin sama da 1,000, da cibiyoyin hada-hadar kuɗi, ƴan kasuwa da jami’an gwamnati, inda aka nuna yadda bashi zai taimaka wa mata ƴan kasuwa, matasa da masu sana’o’in sufuri.

Babban Daraktan CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya ce lamunin masu amfani da kayayyaki bai kamata ya zama gata ga wasu mutane kaɗan ba, sai dai ya kamata ya kasance dama ga duk ƴan Nijeriya masu aiki.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

Kamfanin ya kuma bayyana cewa ya taimaka wajen samar da lamunin da ya kai sama da Naira biliyan 53.5 ga mutane sama da 351,000, tun bayan fara aikinsa, inda mata suka kai kusan kashi 59 cikin 100 na waɗanda suka amfana.

Ana sa ran tsarin SPARK zai samu karɓuwa a faɗin Nijeriya kafin ƙarshen shekarar 2026.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno
  • Abubakar Sulaiman
    Mahara Sun Kai Hari Shingen binciken Sojoji, Sun Kashe Soja Ɗaya A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

MASU ALAKA

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC
Manyan Labarai

November 1, 2026
Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

November 1, 2026
Mahara Sun Kai Hari Shingen binciken Sojoji, Sun Kashe Soja Ɗaya A Filato
Labarai

Next Post
Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

November 1, 2026
Sin Ta Fitar Da Cikakken Tsarin Sauka A Duniyar Wata

Sin Ta Fitar Da Cikakken Tsarin Sauka A Duniyar Wata

November 1, 2026
Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

November 1, 2026
Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

November 1, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba

November 1, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Ranar Biranen Duniya

Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Ranar Biranen Duniya

November 1, 2026
Mahara Sun Kai Hari Shingen binciken Sojoji, Sun Kashe Soja Ɗaya A Filato

Mahara Sun Kai Hari Shingen binciken Sojoji, Sun Kashe Soja Ɗaya A Filato

November 1, 2026
An Fitar Da Kudurin Kwamitin Kolin JKS Dangane Da Jagorancin Jamiyyar

An Fitar Da Kudurin Kwamitin Kolin JKS Dangane Da Jagorancin Jamiyyar

November 1, 2026
Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

November 1, 2026
Manzon Musamman Na Shugaba Xi Jinping Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Wasannin Olympics Na Matasa A Dakar

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci