Kasar Sin ta tsara harba rokoki biyu zuwa duniyar wata, karkashin shirinta na binciken duniyar wata, yayin da shirin tabbatar da nasarar aikin ke gudana yadda ya kamata.Da yake tabbatar da hakan a jiya Asabar, yayin taron karawa juna sani karo na bakwai da ya gudana a birnin Beijing, babban injiniya, kuma mataimakin babban mai tsara naurori, karkashin shirin binciken duniyar wata na yan sama jannati na kasar Wang Xiang, ya ce an tsara harba naurar sauka kan duniyar wata ta Lanyue, da kuma kumbon dakon yan sama jannati na Mengzhou, domin sauka a dairorin da aka tsara, inda sassan biyu za su kewaya su kuma hade da juna a dairar wata.
Daga bisani kuma yan sama jannatin za su fito daga kumbon Mengzhou su shiga naurar Lanyue, wadda za ta sauke su a doron duniyar wata domin gudanar da ayyukan binciken kimiyya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)













