Sojojin Nijeriya da ke ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai sun kashe wasu manyan mayaƙan ƙungiyar ISWAP, ciki har da wani mamba a majalisar Shura ta ƙungiyar mai suna Abu Hajara, da wani babban kwamanda mai suna Abul Walid, a yayin artabu a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Harin ya faru ne ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, bayan mayaƙan ISWAP sun kai hari kan sansanin sojojin da ke yankin. Dakarun ƙasa sun mayar da martani tare da samun taimakon jiragen yaƙi na rundunar sojin sama, inda suka yi nasarar fatattakar maharan tare da kashe wasu daga cikinsu.
Sanarwar da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa Abul Walid na daga cikin manyan kwamandojin ISWAP, kuma yana da kusanci da Ba Shuwa, wanda ake bayyanawa a matsayin babban jagoran ƙungiyar a yankin Tafkin Chadi. An kuma kashe wasu mayaƙa biyu Larabawa da aka bayyana a matsayin manyan jami’an ƙungiyar.
Bayan artabun, sojojin sun kwato makamai da alburusai da dama, tare da na’urorin sadarwa da mayakan suka arece suka bari. Rundunar ta ce wannan nasara na daga cikin ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta’adda domin rage ƙarfinsu da tarwatsa tsarin shugabancinsu.
Wannan artabu ya zo ne kwanaki uku bayan wani hari da aka kai wa sojoji a Buni Yadi, inda rundunar sojin ta ce ta kashe mayakan Boko Haram/ISWAP 55, ciki har da wasu manyan kwamandojin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Rundunar ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da ayyukan yaƙi da ta’addanci domin kare al’ummar yankin Arewa maso Gabas.














