Assalamu Alaikum. Mutum ne yake ba da kudin Gero ga manoma tun kafin ma amfanin ya girma. Misali, in ana saida Gero a lokacin shifka #450, to sai su yi lissafi a kan tsammanin Geron zai sauko zuwa #150. Ka ga duk #450 da ya ba manomi, zai kawo mai Tiya 3 ta Gero kenan. Mene ne halaccin wannan ciniki?
Wa alaikum assalam, Ya halatta mutukar sun cimma daidaito a kan hakan, wannan shi ake kira Salam a wajen malaman Fikhu (Kan ta gasu), Annabi (SAW) da ya zo Madina ya samu mutanen garin suna wannan cunikayyar, sai ya ce musu: (Duk Wanda zai yi, to ya yi a cikin Ma’auni sananne, zuwa lokaci sananne).
Allah ya halatta wannan nau’i na cinikayya saboda saukaka wa mutane, Manomi zai iya bukatar kudi kafin amfaninsa ya zo.
Allah ne mafi sani.