ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kasar Sin Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Ta Hanyar Ingiza Samun Wadata Ba Tare Da Barin Kowa A Baya Ba

by CMG Hausa
4 years ago
Kasar Sin

Abin dake shaida wadata da karfin wata kasa shi ne karfinta na kawar da talauci, kuma shaidar karfin wata gwamnati shi ne matakan da ta dauka don rage gibin dake tsakanin mawadata da matalauta.

Tabbatar da samun wadata ba tare da barin kowa a baya ba, daya ne daga cikin wasu muhimman abubuwa dake cikin tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin. Mawadata su taimakawa matalauta wajen fita daga talauci, wata hanya ce mai kyau ta tabbatar da wannan buri.

  • Gidauniyar Masari Ta Tallafa Wa Marasa Karfi A Jihar Katsina

Ni ne na yi sa’a sosai, saboda iyali na daya ne daga cikin iyalan da suka samu matsaikaciyar wadata a matakin farko, amma a wancan lokaci, wato waje yau shekaru 30 da suka gabata, a lokacin da nake karatu a makarantar firamare, ban san cewa akwai wasu mutane da suke fama da talauci mai tsanani a yankunan karkara ba.

ADVERTISEMENT

Kasar Sin

Wata rana, makarantar da nake karatu ta kai mu wani kauye, don sanin yadda manoman kauye suke da zama, sannan mu ba su wasu kayayyakin jin kai.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Wanda na baiwa taimako shi ne wani yaro mai shekaru daidai da nawa, ya kuma gaya min cewa, a baya ya dauka cewa, ba zai iya kammala karatun firamare ba sai dai ya nemi wani aikin yi domin taimakawa iyayensu fama da talauci, daga baya gwamnatin wurin ta ba iyalinsa wasu kudin tallafi, shi ya sa ya koma makaranta, zaman rayuwar gidansa ma ya samu kyautatu.

A waccan lokaci, ni karamar yarinya ce, ba ni da karfin taimaka masa, amma na san cewa, ina da nauyin dake bisa wuya na a nan gaba, wato dole ne na taimakawa sauran mutane dake fama da talauci idan na samu arziki.

Wani dan jarida ya ga ni da wancan yaro muna rubutawa juna adireshenmu, sai ya tambaye ni dalili, na ba shi amsa cewa, na sa niyyar ci gaba da taimake shi nan gaba. Na yi imanin cewa, duk daliban da suka halarci wannan aikin da makarantarmu ta tsara, za su fahimci ma’anar samun arziki tare, kuma za su sauke nauyin dake wuyansu na taimakawa wadanda suke bukata nan gaba.

Kasar Sin
Gudanar da irin wannan aiki a cikin makaranta, hanya daya ce daga cikin matakan da gwamnatocin matakai daban daban na kasar Sin su kan dauka, na ilmantar da yara sanin taimakawa duk wanda yake bukata.

Masanin kasar Birtaniya Martin Jacques ya taba nuna cewa, babban sauyin da Sin take saukewa ya wuce tunanin mutanen yammacin duniya. Martin Jacques ya fadi gaskiya, tun lokacin kafuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin zuwa lokacin kaddamar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, har zuwa sabon zamani na gina zaman al’ummar gurguzu mai sigar halayen kasar Sin, gwamantin kasar Sin ta kan sanya moriyar fararen hula a gaban kome, ba ta taba mantawa da kowa ba.

Kasar Sin ta samu ci gaba da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba, wannan shi ne niyyar JKS ta samarwa dukkan jama’arta zaman rayuwa mai arziki.

A ganin Martin Jacques, Sin tana daidaita matsalar rashin adalci ta hanyar aiwatar da manufar samun arzik tare, abin da manyan kasashen yamma har yanzu ba su cimma nasara ba tukuna. Kawar da rashin daidaito da rage gibin mawadata da matalauta nauyi ne dake wuyan duk wata gwamnati, kuma ya zama dole ga kowace gwamnati.

Amma lokacin da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da irin wannan mataki, wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma sun shafa mata bakin fenti wai cewa, gwamnatin Sin na kara karfin mallaka.

Idan gwamnatoci biyu da suke kasancewa a gaban jama’a a lokaci daya, wata daga cikinsu ta yi alwashi kawai a maimakon kokarin cika alkawari, amma wata daban ta kan dauki nagartattun matakai wajen kawar da talauci, da ba da taimako ga wadanda suke domin kokarin cika alkawarinta, ku gaya mana wace kuke so ko kuke bukata? (Amina Xu)

Kasar Sin
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
‘Yan Daba Sun Farmaki Mai Taimaka Wa Ganduje Na Musamman A Kano

'Yan Daba Sun Farmaki Mai Taimaka Wa Ganduje Na Musamman A Kano

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.