A ranar Asabar din nan ne ake bai wa mai martaba Sarkin Bwari, Alhaji Awwal Musa Ijakoro sandan girma.
Bikin bayar da sandan girman wanda Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Mohammed Musa Bello zai shugabanta, zai gudana ne a Cibiyar Bunkasa Al’amuran Mata da ke Kuduru a yankin Bwari da ke Abuja.
Wanda ake sa ran farawa daga karfe 11 na safe, bikin zai samu halartar manyan baki da suka kunshi sarakuna, shugabannin siyasa da na al’umma da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Shin wanene mai martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro?
Mai girma Alhaji Awwal Musa Ijakoro, wani bawan Allah ne da za a ce al’ummar kasar Bwari da ke Abuja suka yi sa’ar samu a cikinsu kuma har ya zama sarki. Wannan duk yana daga cikin hikimar Allah.
Koda yake ya fito ne daga gidan sarauta tun asali, amma tun kafin ya zama sarki al’ummar kasar Bwari da dama suke girmama shi a matsayin shugaba wanda yeke da tausayin jama’a, kwarjini da ilmin sanin yadda ake zama lafiya da al’umma kamar yadda ya taso ya ga mahaifinsa na yi.
Tarihi ya nuna cewa an haifi mai martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro ne a garin Bwari da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar 9 ga watan Yunin shekarar 1977.
A ranar 24 ga watan Oktobar 2017 ne Ministan Abuja, Malam Mohammed Musa Bello ya nada Alhaji Awwal Musa Ijakoro a matsayin sabon Sarkin Bwari domin ya gaji mahaifinsa, Alhaji Muhammad Musa Ijakoro, da ya riga mu gidan gaskiya a ranar 29 ga Agustan 2017.
A hannun mahaifisa Alhaji Musa Muhammad Ijakoro ne masarautar ta zama mai daraja ta biyu a ranar 12 ga watan Yunin 1997.
Bincike ya nuna daukakar da masarautar tasu ta samu ta biyo bayan umurnin da marigayi shugaban kasa Janar Sani Abacha ya bai wa ministan Abuja na wancan lokacin ne Laftanar Janar Jeremiah Useni, da ya kara daukaka jdarajar masarautun da ke Birnin Tarayya Abuja.
A shekarun da mai martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro ya yi a kan karaga ya samu nasarar hada kan al’umarsa waje guda wanda hakan ya kawo zaman lafiya da daukaka a masarautar baki daya.
Dangane da batun ilmi kuma mai martaba Alhaji Awwal Musa Iajkoro ya yi karatun firamere ne a Suleja a shekarar 1984 zuwa 1989 a makarantar da ake kira Aliyu Wali. Sannan ya yi karatun sakandare a Makarantar GSS Kwali Abuja inda ya kammala a 1997.
Daga 2001 zuwa 2003 mai martaba ya yi karatun difuloma a kan harkokin gwamnati a Jami’ar Abuja wanda daga nan ne aka fara nada shi sarauta.
Ya kuma yi digiri a kan harkokin mulki (B.Sc Public Administration) a Jami’ar Nasarawa da ke Keffi. Kafin zaman sa Sarkin Bwari dai an nada shi Ciroman Bwari.
Ya yi aikin gwamnati musamman a makarantar Shari’a ta Nijeriya reshen Bwari daga 2000 zuwa 2010.
Kamar yadda Jagaban Shere Koro, Bala Ahmad Shere ya taba bayyana wa jaridar Daily Trust, “An daga darajar masarautar Bwari sama da shekara 25 da suka gabata tare da wasu hakimai na Birnin Tarayya Abuja.
Sun hada da Gundumomin Kwali da Kuje da sauran wasu masarautu na dagatai.
“Marigayi Dr. Musa Muhammad Ijakoro ya kasance wani basarake na daban a tsakanin wadanda suka mulki Bwari tun daga 1902 zuwa 1975. Bwari tana da dagatai guda 10 wadanda su ne suke zaben hakimi a Gundumar Bwari. Kuma a cikin wadannan dagatai akwai Koro, kuma akwai Gwari.”
Shi ma da yake jawabi, Ciroman Bwari, Abubakar Musa Ijakoro, ya bayyana cewa, biyo bayan ritayar dole da Gwamnan Soja na Jihar Arewa maso Yamma, Kwamishinan ‘yan sanda, Usman Faruk, ya yi wa Hakimin Bwari, Abubakar Barau Musa Angulu, a tsakanin shekarar 1954 zuwa 1975, an yi dokar soja da ta bayar da umurnin cewa a nada ‘yan asalin yanki a mukaman sarauta a gurabun da aka samar.
Ya ce yayin da aka bayar da damar fitowa domin neman kujerar Hakimin Bwari wadanda suka nema “sun hada da Malam Danladi Zuma – daga Bwari (Gbagyi), Samaila Mainasara – daga Ija-Gbagyi (Gbagyi), Salihu Sunbwada – daga Diko (Gbagyi), da Musa Muhammad – daga Ijakoro (Koro).
Ya yi nuni da cewa yayin da shugabannin kauyen Koro suka gabatar da dan takara daya tilo, sai su Gbagyi suka gabatar da ‘yan takara uku wadanda Ijakoro ya kayar da su.
“A halin da ake ciki, ya kamata duk duniya su sani cewa gundumar Bwari ba kawai ta kunshi Gbagyi da Koro da Hausawa da Fulani ne kadai ba. An kafa Zangon Hausawa na Bwari sama da shekara 89 kafin a tilasta wa Gbagyi su sauko daga tsauni.
“Hakazalika, muna so mu bayyana baro-baro a nan cewa Koro ya yi hijira zuwa Abuja da wuri tun kafin Gbagyi. Bisa ga takardun tarihi, duk inda ka ga Gbagyi, tabbas sun zo ne bayan Koro. Kuma sun girmama Koro. Shi ya sa Gbagyi kawai suke kiran Koro da ‘Apoyi’, ma’ana mai ceton rai.
Sarakunan Koro ne suka yi wa sarakunan Gbagyi rawani, wanda ke nufin sun kasance talakawan Koro a tsawon tarihin masarautar Abuja.
“Kafin zuwan ’yan mulkin mallaka da kuma bayan da Nijeriya ta samu ‘yancin kai a 1960; a koyaushe Dagacin Bwari ne yake nada Sarkin Dogon Kurmi.
Hakazalika, Hakimin kauyen Ushafa ya kasance Sarkin Ijakoro ne yake nada masa rawani,” ya bayyana.
Ciroman Bwari ya kuma ce dukkan abubuwan tarihi ko alamomin da ke Abuja mallakin Koro ne, ba wai Gwari da ke ikirarin mallakin Abuja ba.
Ya yi ikirarin cewa shahararren dutsen Aso Rock da Zuma Rock mallakin Koro ne. “Ko kuwa akwai wani Gbagyi da zai iya yin da’awar wadannan alamomin?” Ya tambaya.
Yayin hada wannan labarin ne kuma muka sami labarin rasuwar mahaifiyar mai martaba Alhaji Awwal Musa, da fatan Allah ya rahamshe ta, Allah ya bai wa mai martaba da sauran iyalanta hakurin jure rashin.