Wani rahoto da aka fitar a Talatar nan, ya nuna cewa ya zuwa karshen watan Yunin bana, adadin masu amfani da fasahar AI mai gudanar da ayyuka a kasar Sin sun zarta miliyan 700.
Kazalika, rahoton na cibiyar lura da harkokin sadarwar intanet na kasar Sin, ya ce wannan salo na fasahar AI ya ratsa kaso sama da 50 bisa dari na al’ummun kasar Sin.
Har ila yau, rahoton ya ce akwai tarin hidimomi da ake samu daga wannan bangare na fasahar AI, muhimmai sun hada da amfani da ita a matsayin abokiyar tattaunawa. Akwai kuma kaso 76 bisa dari na masu amfani da fasahar wajen neman amsar tambayoyi.
Rahoton ya kuma ce an samu matukar karuwar masu mallakar na’urorin sadarwa masu basira, wanda hakan ke nuni ga bukatuwa ga cin gajiyar fasahohi masu basira.
Rahoton ya kuma ce kaso 38.7 bisa dari na masu amfani da intanet sun sayi na’urori masu basari ne ta intanet cikin watanni shida da suka gabata. (Saminu Alhassan)














