Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa zaman lafiya da haɗin kan al’ummar jihar sun taimaka wajen jawo masu zuba jari tare da bunƙasa tattalin arzikinta.
Sule ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Lafia, yayin bikin Nasarawa Carnival da aka gudanar a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekaru 30 da ƙirƙirar Jihar Nasarawa.
Gwamnan ya ce jihar na amfani da albarkatun ma’adinanta wajen jawo masu zuba jari, ciki har da kamfanonin da ke hako tare da sarrafa ma’adinai a cikin jihar.
Ya ce zaman lafiya na daga cikin muhimman abubuwan da masu zuba jari ke la’akari da su kafin su zuba jarinsu, yana mai cewa jihar za ta ci gaba da samun masu zuba jari ne matuƙar akwai zaman lafiya.
Sule ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su gudanar da bambancin ra’ayi cikin mutunta juna yayin da zaɓe ke gabatowa, yana mai cewa bai kamata siyasa ta zama sanadin rarrabuwar kan al’umma ba.
Gwamnan ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa sauye-sauyen tattalin arziki da ya ce suna bai wa jihohi damar ƙara samar da kuɗaɗen shiga, inganta tsaro da kuma samar da wutar lantarki.
Ya kuma bayyana cewa Nasarawa ta amince da ƙudirin kafa ’yan sandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro.
Sule ya taya al’ummar Nasarawa murnar cika shekaru 30, tare da bayyana fatansa cewa jihar za ta samu ƙarin ci gaba a cikin shekaru 30 masu zuwa.














