Ana kiran lambar yabo ta Fields da lambar yabo ta Nobel a fannin lissafi, kuma tana daya daga cikin manyan lambobin yabo na bangaren lissafi na duniya. Ana bayar da lambar yabo ta Fields duk bayan shekaru hudu-hudu ga wadanda suka fi samar da gudummawa a fannin lissafi a duniya kana shekarunsu ba su haura 40 a lokacin ba. Maxim Kontsevich yana daya daga cikin wadanda suka samu irin lambar yabon. A cikin shekaru da dama da suka wuce, ya kiyaye yin mu’amala sosai tare da bangaren lissafi na kasar Sin, da kasancewa manazarci na jami’o’i da hukumomin nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin.
A kwanakin baya, yayin da yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, Kontsevich ya bayyana cewa, yana sha’awar tsarin zamantakewar al’ummar kasar Sin. Kasar Sin ta iya daidaita albarkatu da tsara shirye-shirye da kuma aiwatar da ayyuka, a ganinsa, kasashen yammacin duniya ba su da irin wannan tsarin. A sakamakon tinkarar matsaloli iri daban daban, a halin yanzu zai yi matukar wuya kasashen yammacin duniya su iya aiwatar da manyan ayyuka masu dogon zango. (Zainab Zhang)














