Mutane da yawa sun turo da tambayoyi suna son bayanin hukuncin kebance ranar Juma’a da Azumi idan ta dace da ranar Arfa. Akramakallah a yi mana bayani.
To Dan’uwa Annabi (SAW) ya kwadaitar game da yin Azumi ranar Arfa, inda ya tabbatar da cewa yana kankare zunubin shekaru biyu, Kamar yadda Tirmizi ya rawaito, sai dai ba a son wanda ya je Aikin Hajji ya yi azumin a ranar ARFA, ana so ya shagala da addu’a da zikiri a ranar.
Bukhari da Muslim sun rawaito hadisi daga Annabi (SAW) yana cewa: “Ka da dayanku ya azumci ranar Juma’a ita kadai, sai dai ya hada ta da ranar da take gabaninta ko ranar take kafin ita”.
Bisa Hadisin da ya gabata za mu fahimci idan Arafa ta fado ranar Juma’a abin da yake daidai shi ne mutum ya azumci yinin da yake kafin ranar Arfa tare da ranar, saboda ba zai yiwu ya azumci yinin da yake bayan Arfa ba, tun da ya dace da ranar Sallah, Azumi kuma ranar Sallah ya haramta kamar yadda ya zo a Hadisin Umar Dan Khaddab.
Duk da cewa akwai malaman da suka halatta kebance ranar Juma’a da Azumi idan ta fado ranar Arfa saboda hujjar cewa an hana yin azumi ranar Juma’a ne ita kadai saboda kar a kebance ranar Juma’a da girmamawa.
Wanda Kuma ya yi azumin Arfa ranar Juma’a, ya yi ne saboda Arfa ba saboda girmama Juma’a ba, sai dai azumin Arfa duk girman falalarsa azumi ne na Nafila, kuma Hadisin da ya hana kebance ranar Juma’a da azumi a kan azumin Nafila yake magana.
Duka kwanaki goman farkon Zulhijja kwanaki ne masu girman falala, babu kwanakin da suka fi su daraja a duniya, idan mutum ya azumci ranar takwas ya hada da ranar Arfa yana kan alkairi Maigirma da kabakin lada mai maiko, sannan zai fita daga sabanin malamai, kuma zai samar da nutsuwa a zuciyarsa.
Allah ne Mafi sani.
Yaya Hukuncin Kame Baki Ranar Idin Babbar Sallah?
Shin akwai wata madogara game da kame baki ranar idin babbar sallah ga wanda zai yi layya?
Wa alaikum assalam, Tabbas Tirmizy ya rawaito a hadisi mai lamba ta:542 cewa: “Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya cin wani abu ranar idin layya har sai ya dawo daga sallar idi.” Albani ya inganta shi. Sai dai hadisin bai bambance tsakanin wanda ya yi layya ba da wanda bai yi ba. Ban san wani daili ba ga wanda ya ce sai naman layya za a fara ci.
Allah ne mafi sani.