Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana a Alhamis da shugaban Isra’ila Isaac Herzog bisa bukatar hakan da Herzog din ya gabatar, a gefen taro na 7, na tattaunawa da gina cudanya da kwarin gwiwa a nahiyar Asia.
Wang Yi ya ce batun Palasdinu shi ne tushen matsalar yankin Gabas ta Tsakiya, yana cewa al’ummomin Yahudawa da Palasdinawa na da ‘yancin rayuwa cikin zaman lafiya da kafa ‘yantattun kasashe.
Haka kuma, Wang Yi ya gana da takwaransa na Turkiye, Hakan Fidan a birnin Baku. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














