A wannan makon ne rukunin farko na alhazan Nijeriya da suka gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyya ya iso Nijeriya. Jirgin farko dauke da mahajjata 425 daga Jihar Sakkwato ya sauka a filin jirgin saman Sultan Abubakar da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Talata.
Shugaban kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama na hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Goni Sanda ya bayyana cewa dawo da alhazan zuwa Nijeriya zai kasance ne kamar tsarin farko na jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki, domin yin adalci wajen gudanar da aikin.
- Bukatar Dakatar Da Kara Kudin Wutar Lantarki A Nijeriya
- Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Kasashen Afirka
Wasu daga cikin alhazan Nijeriya da suke kasar Saudiyya yanzu haka da wakilinmu ya zanta da su, sun nuna rashin jin dadinsu da wasu tsare-tsaren da kamfanin da ke kula da abinci da muhallin alhazan ya yi.
Daga cikin manyan matsalolin da alhazan ke fuskanta sun kunshi matsalar rashin abinci mai inganci, muhallin, magunguna da kuma cinkoso, yawaitar rashin lafiya da sauransu.
Da yake karin haske kan matsalolin da aka fuskanta a zaman Mina, shugaban hukumar kula da jin dadin alhazan Nijeriya (NAHCON), Zikrullahi Hassan, ya shaida cewa sama da alhazan Nijeriya 52,000 ne ba su samu wurin kwana ba a yayin tafiyar kwanaki biyar na gudanar da aikin hajji a bana a Mina.
Ya kara da cewa muhalli mai daukan mutum 43,000 ne aka samar wa alhazan Nijeriya 95,000, hakan ya sa sama da alhazai 50,000 ba su da matsuguni tsawon kwana biyar da suka shafe a Mina.
Wakazalika, Bincike ya nuna cewa a bana dai ba a tsaurara matakai na hana duk wani da bai da cikakken izinin shiga aikin Hajji zuwa Mina da Arfa. Hakan ne ya sanya Takari samun damar shiga aikin hajji a Mina da filin Arfa.
Alhazan Nijeriya da dama sun nuna bakin cikinsu bisa rashin samun damar zuwa Raudah (Makwancin Manzon Allah) da ke Madina domin ziyarar Annabi Muhammadu, inda suka nuna hakan a matsayin gazawar hukumomi ko jami’ai bisa rashin samar musu da izini. Duk da sun nuna cewa samun izinin bai da wati wuya idan aka nema ta hanyar da ta dace.
Daya daga cikin alhazan Nijeriya da ke can kasa mai tsarki (zuwa lokacin da aka zanta da shi), ya shaida wa wakilinmu cewa an samu shigar ‘yan Nijeriya mazauna kasar Saudiyya cikin sha’anin aikin hajji wadanda suka kara janyo cinkoson da ya addabi asalin alhazan da suka je can domin sauke farali.
Wata Hajiya daga Jihar Gombe wacce ta bukaci a sakaye sunanta, ta ce, “Gaskiya zamanmu a Mina an samu matsalar rashin wurin kwanciya, bayan gida da kuma abinci domin ba isa yake ba. Haka a otel lamarin yake, a gaskiya ba kowa ke samun abinci ba.”
Hajiyar ta nuna matukar damuwarta kan yadda ta fuskanci matsalar rashin samun magunguna ciwon baya da take fama da shi, inda ta ce sai da ta yi wasu ‘yan dabaru tukunna take iya tafiyar da kiwon lafiyarta.
“Babu abun da ke sanya ni bakin ciki tsakani da Allah kamar yadda ka san ban yi aikin hajjin nan ba haka nake ji, rashin zuwanmu Raudar nan. Na bi, na bi amma lamarin ya ci tura. Na yi magana har ga shugabanni amma hakan ya gagara samuwa. Na jen wurin ma’aikatan Haram (Askar) tare da roke su amma amsar da suke ba mu shi ne lallai sai mun zo da Tasrif wato izinin samun damar shiga ziyarar.
“Tasrif din nan a ina ake samu? Na tambayesu suka ce jami’anmu ne za su samo mana shi. A ina za mu samu mun rasa, muna ji muna gani mutane za su zo su yi layi a wuce da su Raudah amma mu sai dai a bude mana bayan katanga wanda an riga an kewaye babu inda ma za mu gani. A cikinmu wadanda muka zo kusan gaba daya ba mu samu zuwa ziyarar Raudah ba.
“Na san dai wata Hajiya guda daya da ta san wani a Madina, ya zo ya nuna mata hanya ta samu wannan Tasrif din a wayarta ta hakan ta ce min ta samu dama ta kai mutane kusan 50. Kamar ‘yar jarida haka na zama ina ta bibiyar mutane domin na ji ko sun samu zuwa ziyara, kowa ya ce bai je Raudah ba. Wannan rashin ziyarar ya damemu sosai har yanzu haka nake ji.
“Kwananmu uku da rabi a Madina, amma ba mu samu wannan ziyarar ba, gaskiya raina ya baci sosai,” in ji ta.
Shi ma wani Alhaji da bai nemi a sanya sunansa ba, ya shawarci hukumar alhazan Nijeriya da ta sake duba yanayin tsarin abinci da ake bai wa mahajjata, yana mai cewa da yawan lokaci ana bai wa alhazan Nijeriya abincin da ba su saba ci a nan gida Nijeriya ba.
“Sauyin abincin da aka mana ya sanya wasu da dama suka yi ta yin gudawa, domin ba su samu cin irin abincin da ake ba su a nan ba. Amma mun yi ta kai korafi da cewa a rika dan barin irin Tikarin nan ko ma a rinka kawo mana irin abincin nasu, amma ba mu samu ba. Muna fatan za a gyara wannan a gaba ta yadda za a bai wa abinci muhimmanci.”
Har ila yau, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu gwamnonin jihohi suka dauki nauyin wasu alhazan a bana, amma ba su duba matsalar sanya malamai masu bita sosai ba, don haka ne ya nemi cewa jihohi su dinga la’akari da masu fadakarwa domin muhimmancinsu a yanayin aikin hajji.
Ya kuma yi korafin matsalar magani, “Gaskiya idan kana neman magani za ka iya yin kwana biyar ba ka samu magani ba. Amma idan kana cikin mawuyancin hali kam wannan tabbas ana daukan mutum a je a duba shi, to a samar da wadatattun magunguna ta yadda ba ma sai mutum ya shiga mawuyancin halin ba.
“Ni na je neman magani ban samu ba dole sai da na sayi maganin da kudi, abun da ya kamata na saya naira 150 a Nijeriya amma na sayi riyar 30 (Naira dubu shida kenan) ka ga ni zan iya cewa an gaza a bangaren magani,” ya shaida mana.
Wakilinmu ya sake zanta da wani Alhaji, inda ya nuna matsalolin da aka samu da cewa, “Ni daya ne daga cikin alhazan Jihar Gombe wadanda muka biyo hukumar jin dadin alhazai ta kasa. A hakikanin gaskiya mun samu matsaloli na rashin jagoranci. Akwai jagoririn da aka nada mana tun daga wajen bita a Jihar Gombe a kan cewa za su jagorancemu tun daga gida har har mu kammala aikin hajji, amma a hakikanin gaskiya mun samu matsala na wannan, domin ba su cika aikinsu ba. Ba mu samu wani da ya zo ya taimaka mana wajen tafiyar da abubuwa ba.
“Yanzu misali zuwa Raudah, alhazanmu da dama ba su samu zuwa Raudah ba, mutane da dama sun ji zafin hakan. Da mun zo za mu shiga Askar za su ce mana mu je mu nemi jagorinmu za su ba mu takarda, amma kuma ba a mu ba. Duk wadanda ka ga sun shiga, to dubaru suka yi. Kashi 90 na alhazanmu ba su je wannan ziyarar ba.
“Haka da muka zo Makkah wurin Dawafi na sauke umura, aka bar mutane suka je da kansu, mutanenmu da yawa ni na nuna musu saitin Makama Ibrahim, inda za su je su fara dawafi. Mutane da dama ba su san wannan wajen ba, wasu za ka ga sun je saitin wani waje na daban ya ce Allahu akbar ba tare da sun san inda za su fara ba. Ya je ya gama zagaye kawai, wannan rashin masu kulawa ne. Akwai jagororin da aka nada su yi wannan abun, amma gaskiya ba su yi ba.”
Daga bangaren hukumar kula da jin dadin alhazan Nijeriya kuwa, hukumar ta ce, ana daukan matakai wajen shawo kan matsalolin da ake akwai tare da dakile faruwar hakan a nan gaba.
A wani taron da aka yi da masu ruwa da tsaki da masu hidima wa alhazai na kasashen Afrika ciki har da Nijeriya (Mudawwafts) da masu kula da abinci da muhallai a kasa mai tsarki ranar Lahadi, Kwamishinan ayyuka na hukumar jin dadin Alhazai ta kasa (NAHCON), Abdullahi Magaji Hardawa ya shaida cewa, “mun taru ne don mu gabatar da damuwarmu a kan abubuwa da suka faru a yayin zaman da aka yi a Mina, domin an samu kunci sosai a yayin zama da aka yi a Mina da matsaloli da muke ganin ya kamata a magance.
“Alhazan nan sun biya kudadensu ne da cewa za a yi musu hidima, amma an zo an cakuda su da damansu ba su samu wurin zama ba. Da damansu ba su samu abinci ba, an barsu a watse, ba ruwan sha, sannan babu kula mai kyau. Wannan ya bakanta mana rai kwarai da gaske, hakan ya sa mu ga ya dace mu nuna musu bacin ranmu ba za mu amince da hakan ba.
“Kuma duk inda muka samu kwakkwaran hujja na gazawarsu za mu gabatar musu a nemi fansa na wannan abun da aka yi.”
“Ko bara da muka kawo alhazai kusan dubu arba’in da uku ko kusan hakan, an samu wannan matsala ta cinkoso. Aka wayi gari yanzu aka ce dukkanin kasashen duniya an ba su dama su kawo yawan alhazan da ake ba su shekarun baya. A Nijeriya an ba mu dubu casa’in da biyar, kuma a wannan wurin bai canza ba dai don haka karuwar cinkoso za a sake samu.
“Sannan sun ba da dama a kasarsu tun lokacin Umara mutane sun shigo ba su fita ba, sun zauna ne da niyyar su samu su shiga hidimar aikin hajji, hakan ya kara yawan cinkoso. Duk inda ka samu cunkoso a kowani tsarin da ka yi dole ya rushe. Cinkoson nan ya sanya wasu a waje ma suke kwana ko tsafta babu.”
Hukumar jin dadin Alhazan Nijeriya ta nemi amshe ragamar ciyar da alhazan Nijeriya daga hannun Mudawwafts, domin neman wadanda suka dace daga cikin kamfanonin da za a nema.
Hardawa ya ce a shekarun baya suke sanar da bukatar hakan ga kamfanoni su nemi a yayin da jihohi za su zabi masu musu hidimar da suka gamsu da su, amma a yanzu su Mudawwafts sun amshi ragamar amma ba a samu biyan biyan bukata ba.
“Amma yanzu su masu yi hidima wa alhazai su ne suka karbi ragamar kacokam a Mina da Arfa su suke ciyarwa, saboda haka hidimar da yawa, ba wai Nijeriya kadai ba ne kasashe ne masu yawa, kuma a ce wasu ‘yan kalilan ne za su ciyar. Ba kuma lallai ne su zama ‘yan Afirka ba, saboda haka irin abincin da za su dafa ko da su ya musu dadi ba lallai mu ya mana dadi ba, don haka akwai gazawa.
“Amma idan ya zama jihohi su ne suka zabi kamfanin da za suyi musu hidima za su tabbatar an samu wadanda za su dafa abinci irin nau’in wanda suke bukata ta yadda suke so kuma matsalolin za su yi sauki.”
A bangaren matsalolin kiwon lafiya kuwa da aka fuskanta, sha hudu daga cikin mahajjatan Nijeriya 95,000 na bana sun rasu a kasar Saudiyya Arabiyya a kokarinsu na sauke farali. Jagoran tawagar likitocin da ke kula da alhazan Nijeriya, Dakta Usman Galadima, shi ne ya shaida hakan a Makkah yayin ganawa da masu ruwa da tsaki bayan hawan Arfa.
Galadima ya yi bayanin cewa bakwai daga cikin alhazan sun rasu ne kafin hawan Arafa, yayin da kuma wasu shida suka rasu a tafiyar kwanaki biyar (Mashair) na gudanar da aikin hajji, wani guda kuma ya sake rasuwa bayan kammala hawan Arfa.
“Mun samu rasuwar alhazai shida a Masha’ir, hudu kuma a Arfa yayin da wani guda kuma ya rasu a Mina. Kafin nan muna da alhazai bakwai da suka rasu kafin ma ranar Arfa. Yanzu ake kara sanar mana cewa mun kara rasa wani Alhaji guda. Hakan ya sanya zuwa yanzu muna da alhazai sha hudu da suka rasu.
Galadima ya ce an samu bullar cutuka guda uku a yayin aikin Hajji kuma tuni aka kwashe alhazan da suka kamu da cutar domin dakile yaduwar ta. Ya kara da cewa sun samu mata biyu da suka haihu a yayin da suke aikin Hajji a Mina, Arafat da Muzdalifah, daya daga cikin matan ta haihu ne a kan hanya, yayin da dayan kuma aka kaita asibiti ta haihu lafiya lau.
Ya ce, akwai bukatar a sake nazarin duba lafiya kafin tafiya aikin Hajji domin kiyaye lafiya da rayuka.
A cewarsa, hatta mata masu juna biyu an samu a wannan Hajjin na bana, biyu daga Sakkwato, yayin da aka samu daya-daya daga jihohin Adamawa Kwara, Yobe, Filato da Katsina.
Galadima ya kara da cewa an samu masu zubar da ciki biyu, sannan wani Alhaji mai cutar suga aka yanke masa kafa. Ya ce tawagarsa ta duba tare da ba da shawarwari ga alhazan Nijeriya kusan 15,860, yayin da suka tura alhazai kusan 100 zuwa asibitocin Saudiyya domin kyautata kiwon lafiyarsu.