ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙasashen Yankin Sahel 3 Sun Nuna Sha’awar Karɓar Bakuncin Gasar AFCON Ta 2032

by Rabilu Sanusi Bena
2 months ago

Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, mambobin Ƙungiyar Kawancen Ƙasashen Sahel (AES), sun nuna sha’awar haɗa ƙarfi domin karɓar baƙuncin Gasar Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) ta shekarar 2032.

Matakin ya nuna ƙarin haɗin kai tsakanin ƙasashen uku, bayan da aka tabbatar cewa ƙasashen Kenya, Tanzania da Uganda ne za su karɓi baƙuncin gasar AFCON ta 2027, wadda za a buga daga ranar 19 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yuli.

Shirin ya samu ci gaba ne bayan jami’ai daga Mali, Nijar da Burkina Faso sun gana da shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe, a birnin New York domin tattauna yiwuwar shirya gasar tare.

ADVERTISEMENT

A wata sanarwa, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Mali ta bayyana taron a matsayin “babban mataki”, tana mai cewa hakan zai bai wa ƙasashen uku damar fara cika sharuɗan da CAF ta gindaya domin neman karɓar baƙuncin gasar ta 2032.

Idan ƙasashen uku suka samu damar shirya gasar, Mali za ta sake karɓar baƙuncin AFCON karo na farko tun bayan shekarar 2002.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Burkina Faso kuma za ta karɓi baƙuncin gasar a karon farko tun 1998, yayin da Nijar za ta karɓi bakuncin gasar AFCON a karon farko a tarihinta.

A halin yanzu, Mali na da filayen wasa guda biyar da CAF ta amince da su.

Burkina Faso kuma ta samu amincewar babban filin wasanta da ke Ouagadougou a bara.

Ita kuwa Nijar na ci gaba da gyaran Filin Wasa na Janar Seyni Kountché, wanda CAF ta dakatar da amincewarsa da karɓar wasannin ƙasa da ƙasa tun shekarar 2022.

Sai dai duk da wannan yunƙuri, ƙasashen uku na ci gaba da fuskantar manyan ƙalubalen tsaro da suka shafi hare-haren ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

Rabilu Sanusi Bena
+ postsBio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Za’a Dakatar Da Wasa A Farkon Minti 10 Na Kowane Wasa A Kasar Argentina Saboda Girmama Messi
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Ahanor Kan Fam Miliyan 40

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Wadanne Dalilai Ne Suke Sabbaba Karin Karbuwar Sin Tsakanin Al’ummun Duniya?

Wadanne Dalilai Ne Suke Sabbaba Karin Karbuwar Sin Tsakanin Al’ummun Duniya?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.