ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya

by El-Zaharadeen Umar
2 months ago
Kilishi

Garin Kayauki yana da kimanin tsawon kilo mita takwas (8) daga cikin birnin Katsina a kan hanyar zuwa Daura, wannan gari yana cikin karamar hukumar Batagarawa da ke cikin Jihar Katsina kuma nan ne shalkwatar Kilishi ta Katsina

Sana’ar Kilishi na daya daga cikin sana’o’i na iyaye da kakanni, da aka san rundawa ko mahauta da ita a kasar Hausa. Sana’a ce da take da dadadan tarihi wanda har yanzu take tasiri matuka musamman yadda ake amfani da ita wajen girmama baki idan sun kai ziyara wasu wuraren.

Yana daga cikin hali na girmama baki, ka bashi kikishin kayauki ya yi tsarabar da shi, ko kuma idan zaka ziyarci manyan mutane a wasu jihohin Nijeriya ka je masu da kilishi dan kayauki.

ADVERTISEMENT

A Jihar Katsina wannan sana’a ta dade ana yin ta, kuma ta kai wani matsayi da ake amfani da ita wajen girmama bakin da ke zuwa jihar domin gudanar da aiki ko wata hidima da take da aka ka da bukukuwa.

Haka kuma garin Kayauki ya yi shura a sassan Nijeriya da kuma ketare wajen sarrafa Kilishi mai nau’i daban-daban, a iya cewa babu inda sunan Kayauki bai je ba a wannan duniya indai Malam Bahaushe ya taba zuwa.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Babangida Yunusa shi ne shugaban kungiyar masu sana’ar Kilishi ta garin Kayauki, ya bayyanawa wakilinmu yadda ya ga ji wannan sana’a ta Kilishi tun daga Iyaye da kakanni har zuwa yanzu nan, da yake shugabancin kungiyar masu sana’ar Kilishi ta Kayauki a karamar hukumar Batagarawa da ke jihar Katsina.

A cewar sa, wannan sana’a ita ce sana’ar da iyayensu da kakanni su suka yi, har gashi suma sun samu kan su a cikin ta, inda ya ce ada mutanen da ke yin wannan sana’a ba su da yawa, amma yanzu al’umma ne da dama ke cin abinci a cikin ta.

Sana’ar Kilishi ta kai shekaru 70 da fara yin ta a garin kayauki kamar yadda shugaban kungiyar masu sana’ar Kilishi Babangida Yunusa ya bayyana, inda ya ce sana’a ce da ke tattare da rufin asiri kala daban-daban

Ya kara da cewa duk wanda ke sana’ar Kilishi to kuma za ga cewa yana yin wata sana’a daban, inda ya bada misali da cewa hatta dabbobin da suke saye da suke yin Kilishi da su, wani lokaci suna sayar da su idan sun ga riba.

Sannan ya bayyana cewa, suna yin Kilishi na shanu da ragona da kuma kaji, haka kuma suna yin tsomin kuli da aya da dabino da kuma ridi ko nome domin gamsar da  masu sayen tare da ci gaba da rike kambun kayauki da ke samar da kilishi mai inganci .

Shin ya aka yi wannan sana’a ta bunkasa daga wanna gari zuwa wasu garuruwa? Babangida ya ba da amsa da cewa, Jihar Legas da Abuja da Kaduna da kuma Kano su ne manyan abokan huldar su wajen gudanar da wannan sana’a.

Kuma ya bayyana tarihin yin haka ta hanyar baki da ke zuwa Jihar Katsina wani aiki ko taro da ziyara, wanda ya ce a dalilin yin tsaraba da ake tafiya da kilishin su zuwa wasu jahohi ya sa wanna sana’a ta bunkasa zuwa can.

Shugaban ya kara da cewa yanzu saboda zamani wasu abokan hulda ma’ana haduwa da su ne ta hanyar kafofin sada zumunta, kuma ana ci gaba da yin kasuwanci bakin gwargwado

“Sannan zuwa yanzu babu wanda zai iya gaya maka cewa ga inda kilishin Kayauki yake zuwa domin inda bahaushe ke zuwa wannan duniya, to zaka tarar an kai wannan kilishin nan na mu,” in ji shi.

Ya kara da cewa abokan huldar su da ke sauran jihohi kamar yadda ya bayyana sun bunkasa a dalilin wannan sana’a, a jihohi irin su Legas da Abuja da Kaduna da Kano babu inda ba zaka samu kilishin Kayauki ba, duk da cewa suma suna yin na su, amma na Kayauki ya fita daban ya ke.

Shin ko me ya banbanta kilishin Kayauki da sauran kilishin da aka sani, sai ya amsa da cewa, al’umma su ne za su ba da amsa, ba ni ba, domin su ne suka kai shi matsayin da yake yanzu, ya kara da cewa yana da abokiyar hulda a kasar Amurka amma ‘yar Nijeriya ce, duk lokacin da wani zai tafi sai ta turo an saya mata kilishi a wajen sa, harma ta kan yi gargadi da cewa kar a sayo mata kilishi idan ba Kayauki ba.

Alhaji Babangida Yunusa ya ce duk da irin nasarori da ci gaba da bunkasar wannan sana’a ta kilishi da ta yi fice a Kayauki fa, matsalar tsaro da ake fama da ita, ta shafi wannan sana’a ta su so sai, inda ya ba da misali da cewa sakamakon sace dabbobi da barayin daji ke yi yasa dole dabbobin sun yi tsada wanda kuma yana shafar kasuwancin su kai tsaye.

Ya ce ada, kulli akwai wadanda za su yanka shanu na yin kilishi, to amma yanzu abin dan ja baya ba kamar da ba, wanda ya ce suna fatan wannan matsala zata zo karshe abubuwa su dawo yadda suke a ci gada harkoki yadda aka saba.

Shugaban kungiyar masu sana’ar Kilishi ya tabbatar da cewa magana ta yi nisa tsakanin su, da gwamnan Jihar Katsina ta inda suke neman a tallafa masu domin su zamantar da wannan sana’a ta su, inda ya bayyana cewa tuni an dora harsashin wannan ci gaba tun Gwamna Radda yana shugaban hukumar bunkasa sana’o’i ta kasa wato SMEDAN

“Duk wasu shirye-shiryen a wancan lokaci an yi ta yadda za a bai wa mutanen mu tallafi da kuma bashi domin bunkasa wannan sana’a, amma sai aka samu wani tsaiko wanda sai daga baya mu gano inda matsalar take, amma yanzu mun sake yin bitar wannan batun muna san gwamnati ta kara shigowa cikin harkokin sana’ar Kilishi. ” Inji Babangida Yunusa

Ya kara da cewa babban abin da suke so gwamnatin Jihar Katsina ta yi masu a kan wannan sana’a shi ne, ta shigo cikin wannan sana’a wanda kuma alhamdulillah zuwa yanzu gwamnati ta fara amsa kira, tunda har an zo a samar da wurin da za a kafa cibiyar sarrafa Kilishi ta zamani a Kayauki.

A cewar sa, suna amfani da wannan dama su kara tunatar da gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda da ya sake waiwayo kungiyar masu sana’ar Kilishi ta Kayauki wanda daman ya santa, kuma shi uba ne ga kungiyar saboda haka suna da tabbacin bai manta da su ba.

Ya kara da cewa ita wannan kungiya ta su, shi ne ya kafa ta da kansa lokacin da yake SMEDAN shi ne ya buga mata Sitanfi, ya ce suna fatan zai waiwayo su nan ba da jimawa ba domin suma su dandana roman dimokaradiya

Shima da yake karin haske dangane da kokarin da gwamnatin Jihar Katsina ta fara na samar da cibiyar sarrafa Kilishi ta zamani Yahaya Mai Kilishi ya ce sana’ar Kilishi ta taimaka wa kokarin gwamnati na rage masu zaman kwashe wando a jihar baki daya.

Ya kara da cewa jama’ar da ke cin abinci karkashin wannan sana’a ba su da iyaka idan aka duba masu ba da gudunmawa da suka hada da nasu kuli-kuli da barkono da Dabino da Aya da kuma Ridi ko nome duk suna cin abinci a sana’ar Kilishi.

Yahaya mai kilishi Kayauki ya ci gaba da bayanin cewa yanzu haka sama da mutum 30 suna cin abinci a karkashin sa a dalilin wannan sana’a, ya ce idan gwamnati na taimakawa to za a kara samun wadanda za su samu aikin yi a karkashin sana’ar Kilishi.

“Idan gwamnati yat shigo cikin harkokin sana’ar kilishi hakan na iya ba mu dama mu kara bude wasu rassa a sauran jahohi da ke kusa da mu, idan ta kama har wajen Nijeriya ma za mu iya kai kayayyakin mu Insha’Allahu.’ In ji shi.

Ya kara da cewa yanzu haka an ware kadada (Heacter) guda domin samar da cibiyar sarrafa Kilishi a Kayauki wanda ya ce shi da shi aka je wajen da za ayi wannan aiki, saboda haka yana fatan gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda zai sake waiwayo kungiyar su.

Ya ce hatta wadanda za su yi injinan busar da Kilishi na zamani an kawo su, wasu abubuwa ne suka tsayar da shirin wanda yake fatan nan ba da jimawa ba za a cigaba da wannan aiki, wanda ya kara jadadda cewa idan aka taimaki mahauta lallai za a taimaka wajen rage zaman kwashe wando a wannan yanki da ma Jihar Katsina baki daya.

Kilishi
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
NPA Ta Goyi Bayan Yarjejeniyar Shirin Bayar Da Horo Na Musamman Domin Tafiyar Da Tashoshin Jiragen Ruwa

NPA Ta Goyi Bayan Yarjejeniyar Shirin Bayar Da Horo Na Musamman Domin Tafiyar Da Tashoshin Jiragen Ruwa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.