Sana’ar dinki a Zariya babbar sana’a ce da ta zama tushen dogaro da kai, musamman ga matasa da yara ƙanana. Wannan sana’a ta haɗa da ɗinkin kayan maza da mata na zamani dana gargajiya, kuma tana samar da kyakkyawar dama ta kasuwanci. Akwai abubuwa da dama da suka bambanta mutanen Zariya (Zazzau) da sauran al’ummomi. Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali shi ne yadda ake tarbiyyar yara tun suna ƙanana da kuma yadda ake haɗa ilimi da koyon sana’a tun da wuri.
Idan ka ziyarci Zariya, zai yi wuya ka ga yara suna yawo a banza ba tare da abin yi ba. Mafi yawansu ko dai suna makarantar boko ne, ko suna Islamiyya ta zamani, ko kuma suna makarantar allo domin koyon Alƙur’ani da ilimin addini. Idan kuma ba su a makaranta ba, za ka same su a wuraren koyon sana’o’in hannu.
Ɗaya daga cikin sana’o’in da Zazzau ta fi shahara da ita ita ce sana’ar ɗinki. A kusan kowace unguwa za ka samu wuraren koyon ɗinki, inda yara da matasa ke koyon yadda za su dogara da kansu tun suna ƙanana.
Malam Ibrahim Lawal, wanda ya shafe sama da shekara 30 yana koyar da sana’ar ɗinki a Zariya, ya ce al’adar koyon sana’a tun da wuri ce ta taimaka wajen rage zaman banza a tsakanin matasa.
“Yaro idan ya tashi daga makaranta ya zo wajen sana’a, ba ya samun lokacin shiga abubuwan banza. Bayan ya ƙware kuma, sana’ar ce take ciyar da shi har ya iya kula da iyalinsa.”
Shi ma Malam Abdulƙadir Musa, wani mai koyar da ɗinki a Sabon Gari, ya bayyana cewa yawancin waɗanda ya koyar sun bazu zuwa sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasashen makwabta.
“Muna alfahari idan muka ji ɗalibanmu sun kafa sana’a a Abuja, Legas ko ma wajen ƙasar nan. Wannan al’ada ce da ta amfani al’umma sosai.”
A nasa ɓangaren, Alhaji Sani Aliyu, mahaifin yara huɗu, ya ce tun yana ƙarami mahaifinsa ya koya masa cewa ilimi da sana’a su ne ginshiƙan rayuwa.
“Ni ma haka na tarbiyyantar da ƴaƴana. Bayan makaranta sai su je koyon sana’a. Ko da Allah Ya ba su manyan mukamai a gaba, sana’a ba ta taɓa zama abin kunya ba.”
Hajiya Maryam Kabir kuwa ta ce koyon sana’a yana taimakawa yara wajen zama masu ladabi da sanin darajar aiki.
“Yaro idan yana da abin yi, hankalinsa yana wajen ci gaba. Wannan shi ne abin da muka gada daga iyayenmu, kuma muna son ya ci gaba.”
Mustapha Bello, wani matashi mai shekara 22 da ya koyi ɗinki tun yana makarantar sakandare, ya ce sana’ar ce ta biya masa kuɗin karatu har ya kammala jami’a.
“Da ba don sana’ar ɗinki ba, da ban iya ɗaukar wasu nauyin karatuna ba. Yanzu ina da shagona kuma ina koyar da wasu matasa.”
Shi kuma Ahmad Muhammad, wanda ya fara koyon ɗinki yana ɗan shekara 13, ya ce yanzu yana samun abin shiga daga sana’ar tare da taimakawa iyayensa.
“Abin da na koya tun ina yaro shi ne ya zama tushen rayuwata. Yanzu ni ma ina koyar da wasu ƙanana domin su amfana.”
Masu bibiyar harkokin sana’o’in gargajiya na ganin wannan tsari ne ya sa a yau za ka samu maɗinka daga Zariya a ƙasashe irin su Jamhuriyar Nijar, Mali, Algeria, Benin da Burkina Faso, inda suke gudanar da sana’arsu cikin ƙwarewa tare da samar da aikin yi da kuma hidima ga al’ummomin da suke zaune.
Haka kuma, idan aka duba manyan cibiyoyin sana’ar ɗinki a Birnin Tarayya Abuja, za a tarar cewa adadi mai yawa na ƙwararrun maɗinka sun fito ne daga Zariya ko kuma sun samu horo daga guraben koyon sana’a na Zazzau. Wannan ya sa sun kasance cikin waɗanda ake nema saboda ƙwarewa, jajircewa da kuma kyakkyawar mu’amala da kwastomomi.
Baya ga sana’a, har yanzu Zariya na ci gaba da riƙe tsohuwar al’adarta ta koyar da ilimin addini. Akwai makarantun asuba, na rana da kuma na dare, inda yara da manya ke koyon Alƙur’ani da sauran ilimomin addini. Wannan haɗin ilimi na zamani, ilimin addini da kuma sana’a shi ne ya sanya Zazzau ta kasance ɗaya daga cikin garuruwan da suka yi fice wajen gina matasa masu ilimi, tarbiyya da dogaro da kai.
“Wannan al’ada ta Zazzau ta nuna cewa tarbiyya ba ta tsaya kan karatu kaɗai ba, har da koyar da sana’a. Idan aka ci gaba da riƙe wannan tsari tare da inganta shi, zai taimaka wajen rage zaman banza, samar da aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin al’umma”, in ji Malam Muhammad Abubakar wani mazaunin ƙaramar hukumar Sabon Gari.













