A shekarun baya bayan nan, jerin sakamakon binciken jin ra’ayoyin jama’a daga cibiyoyi mabanbanta, na kara shaida karbuwa, da gamsuwar al’ummun duniya game da kasar Sin. A lokaci guda, masharhanta da yawa na ganin ra’ayoyin jama’a na iya zama shaida ta hakika ta tantance tasirin da wata kasa ke kara samu tsakanin sauran takwarorinta.
Sakamakon binciken cibiyoyi daban daban ya nuna sauyi da ake samu a ra’ayoyin jama’a dangane da kasashen duniya masu fada a ji, da yadda matakansu na cudanya da sauran sassa ke haifar da sabon sauyi ta fuskar karbuwarsu.
A jimlace, muna iya cewa sakamakon karbuwa, da yabo da kasar Sin ke samu daga al’ummun kasa da kasa na nuni ga gamsuwarsu da matakan Sin din na cudanya bisa martaba juna, da adalci, da bin tafarkin cimma moriya tare.
Masana da yawa na ganin sauyin, sakamako ne na abubuwa na zahiri da ke wakana ta fuskar tattalin arziki. A yankunan duniya da dama musamman bangarorin kasashe masu tasowa, ra’ayoyin jama’a na karkata ga amincewa da kasashe masu taimakawa wajen cimma muhimman sakamako, kamar dai yadda ake ganin tallafin kasar Sin a bangarorin samar da ababen more rayuwa, da fadada damarmakin cinikayya, da hadin gwiwar raya masana’antu, da zuba jari a muhimman sassan bunkasa kasashe musamman masu tasowa.
Karkashin hakan, muna iya ganin nasarori da kasashe masu tasowa da dama suka cimma na samar da hanyoyin mota, da layukan dogo, da tashoshin ruwa, da cibiyoyin samar da makamashi da fannin raya masana’antu, ayyukan da a zahiri al’ummun irin wadannan kasashe ke gani, tare da cin gajiyarsu kai tsaye.
Bugu da kari, kasar Sin ta wanzar da manufofi masu dogon zango, wadanda suke ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Kuma kasashe masu tasowa da dama na dora muhimmancin gaske kan hadin gwiwa mai dorewa. Don haka Sin din ke samun karin karbuwa tsakanin wadannan kasashe.
A takaice muna iya cewa, yanayin karin karbuwar da kasar Sin ke samu a shekarun baya bayan nan tsakanin sassan kasa da kasa, na da nasaba da manufofin da take aiwatarwa na tallafi, da ingiza ci gaban sauran kasashe karkashin dandaloli da shirye-shiryen hadin gwiwar daban daban, wadanda ke kara kyautata dunkule duniya waje guda, da samar da damarmakin raya tattalin arzikin sassa daban daban na duniya. (Saminu Alhassan)













