Majalisar dattawa ta bayyana cewa majalisar tarayya za ta duba dukkan muhimman abubuwan da suka dace kafin ta ba da shawarar da amincewa da kowanne bukata na kirkirar sabbin jihohi a duk fadin kasar.
Majalisar dattawan ta jaddada cewa, duk da dai wasu ‘yan Nijeriya na nema a kirkiro karin sabbin jihohi, za a kula da batun tare da gudanar da cikakken nazari tare da batun son kai ko bukatu na kashin kai ba.
- Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
- Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka
Mai magana da yawun majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin harkokin kafafen yada labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana hakan a karshen mako yayin da yake magana da manema labarai a gidansa da ke Ilawe-Ekiti cikin Jihar Ekiti. Ya bayyana cewa an riga an karbi kudirin bukatun kirkirar sabbin jihohi har guda 61.
Sanatan, wanda ke wakiltar Yankin mazabar Ekiti ta Kudu, ya tabbatar da cewa za a bi hanyoyin da suka dace kafin a gabatar da kowanne kudiri.
Ya ce, “Zuwa yanzu dai, majalisar dattawa ta karbi kusan kudirorin bukatun kirkirar sabbin jihohi har guda 61. A cikin tattaunawarmu a lokacin sauraren jin ra’ayoyin jama’a a dukkan fadin kasar nan, an dai gabatar da wadannan bukatu a hukumance. Kamar yadda muka bayyana, dukkansu za a duba su da kuma yin kyakkyawan Nazari a kansu.
“Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar.
“Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun.
“Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da suka nema, ba a samu cikakken yarda ba. Dukkan wadannan abubuwan dole ne a yi la’akari da su. Kafin wannan, majalisaun tarayya ba su da hurumin amincewa da kirkirar wata sabuwar jiha.
“Kamar yadda ake ciki a halin yanzu, babu jihar da aka ba da shawara a kirkira. Ba za mu iya tabbatar da rahotanni na karshe ba ko zartar da hukunci kan jin ra’ayin jama’a da aka hada ba har sai an kammala sauraron jin ra’ayin jama’a gaba daya zuwa lokacin da muka dawo,” in ji shi.
Ya jaddada cewa ‘yan majalisar za su ba da muhimmanci ga sha’anin kasa sama da ra’ayoyinsu a yayin yanke shawarar kan batun yin garambawu a kundin tsarin mulkin kasar nan.
“Majalisar tarayya dai wuri ne na yin dokoki da kuma kula da aikin tsarawa ko gyara kundin tsarin mulki. Muna kira ga ’yan’uwanmu ‘yan majalisa su yi amfani da wannan dama da za ta dace ga kowa da kowa.
“Muna maraba da shawarwari daga dukkan ‘yan Nijeriya da suka hada da dattawa da kwararru da shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da kungiyoyin matasa da kungiyoyin mata da kungiyoyin farar hula, har ma da ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje.
“Za a bude taron sauraron jin ra’ayoyin jama’a ga kowa, kuma kundin na karshe kan gyara tsarin mulkin kasar nan zai bayyana batutuwan da ‘yan Nijeriya suka yanke hukunci a kai, ba ra’ayin wata kungiya kadai ba.
“Manufarmu ita ce, tabbatar da duk wasu canje-canje da za a yi a kundin tsarin mulki su kasance mafi kyawu ga bukatar Nijeriya da kuma mutanenta,” in ji Adaramodu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp