Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, ya bayyana sabbin ra’ayoyinsa game da kasuwar kasar Sin, da fasahar kirkirarriyar basira ta AI da kuma mutum-mutumi masu siffar dan’adam, a wata hira ta musamman da ya yi da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG).
A yayin hirar, Musk ya kuma yi magana sosai kan kasar Sin a matsayin wurin zuwa yawon bude ido.A cewarsa, “Kasar Sin tana da ban al’ajabi,” inda ya kara da cewa akwai abubuwa da dama a kasar Sin da suka cancanci zuwa a gan su, wadanda ba za a iya bayyana su gaba daya cikin takaitaccen bayani ba.
Kazalika, Musk ya sake karfafa gwiwar mutane da su ziyarci kasar Sin a duk lokacin da suka samu dama, yana mai cewa, “Idan lokaci ya ba da dama, tabbas a tafi kasar Sin don ganin abubuwan da ke can.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)













