ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 3, Rami Ya Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adinai 4 A Filato

by Sadiq
4 hours ago

‘Yan bindiga sun kashe wasu ‘yan sa-kai uku a ƙaramar hukumar Mangu, yayin da wasu mutane huɗu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba suka mutu bayan wani rami ya rufta a ƙaramar hukumar Bokkos.

An ruwaito cewar ‘yan bindigar sun yi wa masu ‘yan sa-kan kwanton-ɓauna ne a daren ranar Talata, da misalin ƙarfe 9:39 na dare, a yankin da ke tsakanin Kyikyau da Gyambwas, a gundumar Mangu Halle ta ƙaramar hukumar Mangu.

Ƙungiyar Matasa ta Mwaghavul (MYM) ta ce harin ya faru ne a lokacin da dokar hana fita daga magariba zuwa safiya ke ci gaba da aiki a wasu sassan jihar.

ADVERTISEMENT

Waɗanda aka kashe sun haɗa da Samson Dachet, mai shekara 45; Gambo Fwangyil, mai shekara 50; da Zughumnan Bamaiyi, mai shekara 35.

Daraktan Hulɗa da Jama’a na MYM, Tubwot Joël Sunday, ya ce mutanen na cikin waɗanda ke gadin al’ummarsu lokacin da ‘yan bindigar suka kai musu hari.

LABARAI MASU NASABA

El-Rufai Ya Magantu Kan Abokansa Da Suka Yi Shiru Yayin Da Yake Tsare A Hannun ICPC

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanai A Sakkwato

Ya yi Allah-wadai da harin tare da kira ga gwamnatin jihar da ta sake duba yadda ake aiwatar da dokar hana fita a Mangu.

A wani labarin kuma, mutane huɗu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne sun mutu bayan wani rami ya rufta kansu a garin Tangur, da ke ƙaramar hukumar Bokkos.

Wani mazaunin yankin, Maren Jacob, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:20 na rana ranar Talata.

Ya ce mutanen suna haƙar yashi ne a kusa da wani kogi lokacin da ramin ya rufta kansu.

A cewarsa, ‘yan uwansu ne suka fito da gawarwakin domin yi musu jana’iza.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

MASU ALAKA

Kotu Ta Umarci A Kamo Mata Dogarin Gwamna El-Rufa’i
Manyan Labarai

El-Rufai Ya Magantu Kan Abokansa Da Suka Yi Shiru Yayin Da Yake Tsare A Hannun ICPC

September 24, 2026
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato
Manyan Labarai

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanai A Sakkwato

September 24, 2026
Sultan
Manyan Labarai

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

September 23, 2026
Next Post
Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Umarci A Kamo Mata Dogarin Gwamna El-Rufa’i

El-Rufai Ya Magantu Kan Abokansa Da Suka Yi Shiru Yayin Da Yake Tsare A Hannun ICPC

September 24, 2026
An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka

An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka

September 24, 2026
Sin Na Aiwatar Da Kwararan Matakan Ingiza Ci Gaban Duniya

Sin Na Aiwatar Da Kwararan Matakan Ingiza Ci Gaban Duniya

September 24, 2026
Firaministan Sin: Karfafa Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Da Masu Ci Gaba A Fannin Cinikayyar Fasahohin Zamani

Firaministan Sin: Karfafa Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Da Masu Ci Gaba A Fannin Cinikayyar Fasahohin Zamani

September 24, 2026
Xi Jinping Ya Isa Washington DC Don Ziyarar Aiki a Amurka

Xi Jinping Ya Isa Washington DC Don Ziyarar Aiki a Amurka

September 24, 2026
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanai A Sakkwato

September 24, 2026
Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

September 24, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 A Jihar Filato

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 3, Rami Ya Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adinai 4 A Filato

September 24, 2026
Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026
Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.