Connect with us

RAHOTANNI

Nasarorin Gwamnatin Buhari A  Cikin Shekaru Biyar

Published

on

Tattalin Arziki

Noma:

.           Shirin bayar da rance ga manoma na, Anchor Borrowers Programme (ABP), wanda babban bankin Nijeriya ke bayarwa, wanda kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2015, shirin ya bayar da damar cin gajiyar sama da naira bilyan 200 wanda kuma sama da kananan manoma milyan 1.5 masu noma kayayyakin amfanin gona daban-daban daban-daban da suka hada da shinkafa, Masara, Alkama, Auduga, Rogo, Kiwon Kaji, Waken Soya, Gyada da Kiwon Kifi, wadanda ake nima su a kan filin da ya daranma hekta milyan 1.4.

.           Shirin kuma na ABP ya bunkasa noman shinkafa sosai, wanda har ya ninka abin da ake nomawa da cashewa tsakankanin shekarar 2015 zuwa 2019.

.           A tsakanin shekarun 2016 zuwa 2019, an kafa sabbin masana’antun casan shinkafa har guda 10 a kasar nan, sa’ilin kuma da aka kara fadada wadanda ake da su a baya, a yanzun haka kuma ana kan aikin gina wasu sabbi masu yawa.

.           Nijeriya ta kuma zuba jarin sama da dala bilyan guda a kan abin da ya shafi noman Shinkafa alkama Sukari kiwon kaji samar da abincin dabbobi samar da takin zamani da sauransu tun daga shekarar 2015.

.           Majalisar zartaswa ta kasa ta kuma amince da shirin nan na samar da manyan injunan aikin noma na zamani a wannan shekarar ta 2020, shirin mai taken, ‘Green Imperatibe,’ na hadin gwiwa ne da gwamnatin kasar Brazil.

Shirin Musamman Na Shugaban Kasa Domin Samar Da Takin Zamani

.           Wannan shiri ne na musamman da aka kaddamar da shi a shekarar 2017 a mataki na gwamnati da gwamnatin kasar Morocco.

.           Tun daga lokacin kaddamar da shirin a shekarar 2017, an samar da sama da metric tan milyan guda. Hakan yana nufin an samar tare da rarraba sama da buhunan takin zamani na NPK masu nauyin kilo 50 sama da milyan 18 a cikin shekaru uku da fara aiwatar da shirin..         An farfado da masana’antun hada takin zamani guda 22 wadanda suke iya samar da sama da 2.5mt na takin zamanin wanda hakan ne ya kawo faduwar farashin na takin zamanin daga naira 9000 zuwa naira 11000 a kan kowane buhun takin zamanin guda zuwa naira 5500 kacal.

.           An sami damar yin tsimin sama da dalar Amurka milyan 150 ta hanyar daina shigowa da takin zamanin daga wajen kasar nan da kuma samar da shi a nan cikin gida.

.           An kuma yi tsimin tallafin naira bilyan 50 da ake yi a kan takin zamanin a duk shekara.

Saukaka Hanyoyin Kasuwanci

Tallafa wa masu matsakaita da masu kananan masana’antu

Wannan gwamnatin ta kaddamar da wasu hanyoyi masu yawa na bayar da tallafi ga masu kanana da matsakaitan masana’antu a kasar nan.

.           An kaddamar da sabon bankin bunkasa masana’antu wanda aka kafa shi a bisa tsabar dalar Amurka bilyan daya da digo uku, 1.3, (daidai da naira bilyan 396.5) domin bai wa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa basuka masu dogon zango.

.           Tun daga lokacin kafa shi a shekarar 2017, bankin ya bayar da tallafin basukan sama da naira bilyan 100 a fannonin shirye-shiryensa guda 27 wanda sama da ‘yan kasuwa 100,000 suka amfana da shi.

.           Kashi 52 na basukan da bankin ya bayar a shekarar 2019 duk matasa da mata ‘yan kasuwa ne suka ci gajiyarsa.

.           Bankin bunkasa masana’antu ya bayar da bashin sama da naira bilyan 400 ga manya, matsakaita da kananan masu masana’antu na kasar nan tun daga shekarar 2016.

.           Hakanan bankin ya kuma bayar da bashin sama da naira bilyan Biyar a matsayin wani shirin ma’aikatar bunkasa karafa da albarkatun kasa domin habaka ayyukan tono albarkatun kasa a kasar nan, da kuma wasu dala milyan 20 da bankin ya samar domin tallafa wa matasa a fannin kimiyya da fasaha.

.           Shirin Gwamnati na bayar da tallafin saukake halin rayuwa kamar yanda zai zo a nan kasa.

Nasararorin da wannan shirin na saukake hanyoyin kasuwanci ya samar:

.           Aikin majalisar musamman ta shugaban kasa a kan samar da hanyoyin saukake hanyoyin kasuwanci wanda shugaban kasa ya kaddamar da majalisar a watan Agusta na shekarar 2016, da kuma sakatariyar saukake hanoyin yin kasuwanci (EBESI) ya sanya Nijeriya ta taka mataki na 39 na kasashen Duniya wadanda kasuwanci yake da sauki a cikinsu a cikin shekaru uku wanda aka yi hukunci da cewa Nijeriya tana daya daga cikin kasashe 10 wadanda tattalin arzikinsu yake saurin habaka.

.           Hukumar kula da zuba jari ta kasa (NIPC), a shekarar 2017 ta kammala dogon aikin nan nata na tantancewa da duba lissafin ayyukanta, wadanda ‘yan Nijeriya za su amfanu da su, wanda kamfanonin da suka sami amfanuwa da su za su sami hutun akalla shekaru uku zuwa shekaru biyar. An yi tantancewar ne a bayan shekaru 10 da yin na bayansa.

.           Majalisar ta NIPC ta wallafa cikakken bayanin dukkanin hanyoyin zuba jari, wanda hakan ya maishe shi mai sauki ga dukkanin masu sha’awar zuba jarin da su sami dukkanin bayanan da suke nema a kan hakan.

Wasu daga cikin nasarori da ci gaban da shirin na saukake hanyoyin kasuwanci ya samu sun hada da:

.           Sanya hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a kan dokar nan ta kudi ta shekarar 2019. Dokar kudin ta shekarar 2019, ita ce ta farko da ta shaidi Nijeriya a tafarkin farfado da harkokin kasuwanci. Kasafin kudin shekarar 2020 shi ne na farko a cikin shekaru 12 da Nijeriya ta sami nasarar komawa bisa tafarkin shekar kudin da ke farawa daga watan Janairu zuwa watan Disamba.

.           Kirkiro sashen kididdiga (NCR), ko kuma sashen tantancewa da yin rajistar kayayyakin da za a iya dauka daga nan zuwa can wanda babban bankin Nijeriya ya kafa a watan Mayu na shekarar 2016. Wannan sashen ya bai wa kananan ‘yan kasuwa damar samun basuka ta hanyar bayar da jinginan kayayyakin da ake iya motsa su, kamar injuna, dabbobi da makamantansu a matsayin abin da za a iya bayar da jinginarsa. Ya zuwa karshen watan Yuni na shekarar 2018, shafin yanar gizo na wannan shirin ya yi rajistar harkokin kasuwanci guda 630, tun daga lokacin fara shirin a shekarar 2016 zuwa watan Afrilu na shekarar 2020. Wadannan harkokn kasuwancin sun bayar da jinginan kayayyakin da za a iya motsa su har guda 65,370, a shafin na yanar gizo, wanda duk na wadanda suka ci bashin abin da aka kimanta da tsabar naira Triliyon 1.26.

.           Samar da hakkin yin rajistan sunan kasuwanci, neman yin rajistan takardu, biyan kudaden rajista, samar da lambar shaidan biyan kudin haraji da kuma biyan kudaden harajin gwamnatin tarayya.

.           Kaddamar da shirin nan na bayar da biza a bayan an iso cikin kasar nan ga ‘yan kasuwa da sauran ‘yan kasa.

Fensho

A watan Janairu na shekarar 2019 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin nan na biyan kudaden fensho, wanda ya bayar da damar mutum a kan kansa ko kuma ma’aikatun da suke da akalla ma’aikata guda uku da su rika yin tsimin wani abu domin cin gajiyarsa a lokacin da suka yi ritaya daga bakin aikin su ko kuma suka sami wata nakasa.

.           Gwamnatin shugaba Buhari ta bayar da mahimmanci a kan biyan basukan kudaden fensho wadanda masu karban fensho na yanzun da kuma na hukumomin gwamnatin tarayya suke bi.

.           Gwamnatin tarayyar ta saki jimillan naira bilyan 54 domin biyan dukkanin basukan kudaden fensho na kashi 33. Kashi 33 wanda masu karban fensho din suke bi tun daga shekarar 2010 da aka yi karin mafi karancin albashi a wancan lokacin zuwa naira 18,000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan kasar nan.

.           Kamfanin mulmula karafa na Delta; wanda aka jinginar da shi tun a shekarar 2015, a halin yanzun masu karban fensho 3542 na kamfanin duk suna cikin rajistar masu karban kudaden fensho a kowane wata wanda hakan ne ya kawo karshen shekaru 13 da suka shafe suna faman jiran tsammani.

.           NITEL: Sama da ma’aikata 9216 na masu karban fensho a kamfanin a yanzun suna cikin rajistan masu karban fensho wanda hakan ya kawo karshen shekaru sama da 10 da suka shige ba tare da samun hakkokin na su ba.

.           Jami’an ‘yan sanda a rusasshiyar jamhuriyan Biyafara (wadanda aka sallame su daga aiki a shekarar 1971 bayan kare yakin basasa, wadanda kuma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi masu afuwa a shekarar 2000). An biya jimillan naira milyan 571 ga jimillan mutane 174 da suka amfana a watan Oktoba na shekarar 2017.

.           Kamfanin Jiragen sama na kasa: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi umurni da sakin tsabar naira bilyan 24 a watan Satumba na shekarar 2018 domin biyan kashi 50 na ma’aikatan da aka sallama a lokacin da aka durkusar da kamfanin Jiragen saman a shekarar 2003 zuwa 2004.

Kwato kudaden fensho: Hukumar kula da biyan kudaden fensho ta (PTAD), ta kwato tsabar kudade da kadarori da jimillansu ya kai naira bilyan 16 wadanda suka sagale a kamfanonin inshora da wasu sassan.

Harkokin kudi, Kasuwanci Da kare kadarori

.           Kaddamar da sabuwar lambar tsarin masu biyan haraji shekarar 2019. A karo na farko da Nijeriya ta mallaki matattarar tara bayanan dukkanin masu biyan haraji guda daya ga daidaiku da kamfanoni a duk Jihohin kasar nan.

.           Wannan sabon tsarin ya haifu ne a sakamakon hadin kan da ke tsakanin hukumar biyan haraji ta kasa FIRS da kuma hukumomin tara harajin cikin gida na Jihohi ta hanyar yin musayar bayanai da kuma tara ayyukan wajen adana bayanan a waje guda da sauran su.

.           Sabon tsarin yin rajistan ya bayar da dama ga masu biyan haraji a wurare masu yawa kamar hukumar yin rajista ta kasa (CAC), Bankuna ta hanyar yin amfani da lambobin tantancewa da bankuna suke amfani da ita, lambar shaidar zama dan kasa NIMC da sauran su.

.           Inganta danganta a tsakanin hukumar tara kudaden harajin ta kasa da kuma sauran hanyoyin tara kudaden ya samar da damar kara bunkasar kudaden harajin da gwamnati ke Tarawa ya zuwa watan Disamba na shekarar 2015 ya zuwa milyan 35 a karshen shekarar 2018, har ya zuwa abin da ake tsammanin cimmawa a karshen shekarar 2019.

Kasuwanci

.           Kafa ofishin kula da harkokin kasuwanci wanda tawagar kula da tattalin arziki ta yi. Kwamitin ya samar da cikakken bayani a karo na farko na tattara bayanin dukkanin harkokin kasuwanci a karo na farko a tarihin Nijeriya. Cikakken rahoto a kan duk wata harkar kasuwanci da yarjejeniya da Nijeriya ta kulla.

.           Batun yarjejeniyar musayar kudi a tsakanin bankin China da babban bankin Nijeriya : A ranar 27 ga watan Afrilu 2018, babban bankin Nijeriya ya sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta tsawon shekaru uku da ta shafi yin musayar kudi a tsakanin babban bankin na Nijeriya da kuma bankin al’ummar kasar ta China, wanda ya kai jimillan kudin kasar na China bilyan 15, wanda ya yi daidai da naira bilyan 720,00 ko kuma dalar Amurka bilyan 2.5.

Kasafin Kudi

Gabatar da kasafin kudi wanda aka saba gabatar da shi hannu da hannu a cikin littafi ko kuma makale a cikin flash, a halin yanzun ya koma abu da ake gabatar da shi ta hanyar zamani yanar gizo, ta hanya guda ta samar da dukkanin bayanan gwamnati tun daga shekarar 2018. Sabuwar hanyar gabatar da kasafin kudin wacce aka inganta ta haifar da yin komai a fayyace kuma a bisa inganci a tsarin na kasafin kudi.

.           Dawo da tsarin shekarar kasafin kudi daga watan Janairu zuwa watan Disamba, a wannan kasafin kudin na shekarar 2020, karo na farko a cikin shekaru 12.

Sashen Shigi Da Fici

Kafa cibiyar tattara bayanai da bincike ta (MIDAS), wacce ke daidai da irin ta na zamani a tsarin tsaro na tafiye-tafiyen manyan kasashen Duniya, a manyan filayen Jiragen sama na Nijeriya wanda aka fara tun a shekarar 2019 tare goyon baya da hadin kan manyan cibiyoyin tafiye-tafiye na Duniya.

.           An hada cibiyar ta MIDAS da cibiyar binciken masu aikata laifuka ta ‘yan sandan Duniya da sauransu. Hakan kuma ya samar da cikakken bayanai a tsakankanin dukkanin manyan filayen Jiragen sama na Nijeriya da kuma hedikwatar hukumar shigi da fici ta kasa NIS, a Abuja. Hakan kuma ya samar da hanyar tattara bayanan a cikin hanzari kuma ingantattu, tare da samar da hanyar tabbatar da cewa babu wasu mutanan da suka shigo Nijeriya ta filayen Jiragen saman wadanda za su iya haifar da wata matsala a cikin kasar nan.

.           A tare da kafa cibiyar ta MIDAS an kaddamar da sabon tsarin na shekarar 2020 wanda hukumar shigi da ficin ta kasa kaddamar, a matsayin wani mataki na shirin shekaru biyar kan farfado da tsaron kan iyaka daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023.

Sabon Tsarin bayar da Bizan ya kunshi abubuwa kamar haka:

.           Fadada shirin bayar da bizan daga 6 zuwa 79, ta yanda zai dace da yanayin bukatar matafiyan kasar nan.

.           Kaddamar da bayar da biza ta yanar gizo wanda ya kunshi dukkanin bayanan masu dauke da bizan. An alkanta wannan tsarin ne da shirin na MIDAS.

.           Samar da hanyar biya da bayar da bizan ta yanar gizo domin a rage wahalar saduwa da juna jiki da jiki da kuma zargin yin almundahana.

.           Tsarin bayar da bizan a lokacin da baki suka shigo cikin kasar nan an fadada shi ga dukkanin kasashen Afrika wanda aka fara tun a watan Janairu na shekarar 2020.

Kare Hakkin masu saye

A shekarar 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya hannu a kan dokar nan da ta kafa hukumar kare hakkin masu saye (FCCPC), wacce ita ce ta farko a tarihin Nijeriya wacce ta mayar da hankali a kan kare hakkin masu siye a cikin kasar nan.

Biyan Basuka

Daga shekarar 2017 zuwa yanzun, Nijeriya ta bayar da bayanin ta na farko a kan:

.           Biyan basuka a manyan kasuwannin Duniya. Basukan da kasuwannin Duniyar suke bi ya kai jimillan dala milyan 300 wanda ke da wa’adin shekaru biyar. An yi amfani da kudaden ne wajen tallafa wa kasafin kudi na shekarar 2017.

.           Kashi na farko na bashin SUKUK na bashin naira bilyan 100 a shekarar 2017, da kuma kashi na biyu na bashin na SUKUK shi ma na naira bilyan 100 a shekarar 2018, da kashi na uku na bashin na SUKUK na naira bilyan 150 wanda aka kammala shi a kwanan nan a watan Mayu na shekarar 2020. Ana yin amfani da bashin na SUKUK ne wajen aiwatar da wasu mahimman ayyukan manyan hanyoyin kasar nan.

Ilimi

Bayar da tallafi: Gwamnatin tarayya ya bayar da tallafi sama da Naira bilyan 170. A karakshin shirin bayar da ilimi na bai daya(UBE) a dukkanin jhohin Najeriya da baban birnin tarayya Abuja tun daga shekarar 2015. Akwai kuma Naira bilyan 8 a karakshin tallafin ilimin na musamman  a jihohi da kuma bangarorin ilimi masu zaman kansu, ga kuma Naira bilyan 34 da aka tallafawa cigaban malamai a dukkanin jihohin kasar nan da babban birnin tarayya Abuja.

Haka kuma gwamnatain tarayya ta kirkiro wadannan manyan makarantu a kasar nan

 • Jami’ar koyar da albarkatun ruwa ta tarayya da ke jihar Delta
 • Jami’ar sojojin Najeriya a jihar Borno
 • Kwalejojin ilimi guda shida(daya a kowani yankin siyasan kasar nan)

Bayan haka gwamnatin tarayya ta yi kokarin inganta makaratun alamajirai da gwamnatin baya ta gina wajen samar da ingantatun malamai da kuma kayayyakin koyarwa.

 

Kula da lafiya

 • Tallafi ga gwamnatoci jihohi: Kowacce jiha da ma baban birnin tarayya ta sami mafi karancin dalar Amurka milyan 2.5 a karkashgin shirin nan na ceto raywauar mutane milyan daya da ake kira ‘sabing one million libes(SOML) don inganta harkokin lafiya.
 • Asusun bayar da tallafi na lafiya: a karon farko tun bayan gabatar da kudurin nan na lafita na kasa a shekarar ta 2014 , da gwamnatin tarayya ta sanya kasha 1% ala akalla na cikin kudaden shiga wanda aka sami kusan naira bilyan 55 – a kasafin kudin 2015 da aka sanya a asusun tallafawa lafiya. Wanann asusun ya bayar da tallafi wajen samar da kayyakin lafi a daukacin Najeriya ta hanayar shirin nann na kulan da lafiya a matakin farko.
 • Aikawa da majalisar dokokin kasa suka yi, don bai wa hukumar takaitawa yaduwar cututtuka na kasa, NCDC a karaon farko tun bayan kafata a shekarar 2011. Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bai wa hukumar Naira bilyan 5 a watan Maris 2020.
 • Shirin inganta kula da lafiya a kololuwa: An sabunta da inganta asibitocin gwamnatin tarayya da suke ko’ina a kasar nan ta yadda suke iya aikin kula da cutar cancer tare da iya ayyukan manyan cututtuka da suke addabar ‘yan Najeriya. An samar da na’urori mabambanta na zamani a ko ‘ina domin ayyuka a zamance. Babban asibit na kasa da ke Abuja tuni ya amshi na’urorin aikin cutar cancer na zamani guda biyu.

Harkokin kimiyya da fasaha da samar da sababbin damarmaki

 • Najeriya ta sami cigaba matuka ta yadda ta samar da wadannan hukumomi
 • Samar da ingantaccen shiri a kayayyakin da ake sarrafawa a masana’antu wajen samar da cigaban Najeriya na kasa.
 • Samar da tsari a kan fasahar  albarkatun mai na kasa
 • Samar da tsari a kan fatu da sarrafa fatu na kasa
 • Samar da ingantaccen tsari a kan kimiyya da fasaha na kasa
 • Kimiyya da fasaha da samar da sababbin damarmaki daga shekarar 2017-2030
 • Samar da damarmaki ga masana kimiyya da injiniyoyi a Najeriya ta hanyar ofishin kula da fasaha da sana’o’i tare da ingnata su karkashin kulawar ma’akatar kimiyya da fasaha ta tarayya, wanda ya karu daga shida ake ake da su zuwa 57 a shekarar 2019.
 • Shirin nan na mayar da bunkasa bincike harkokin kasuwanci ta wadannan abubuwa
 • Harkokin kasuwancin zuma da man kadai da kilishi da sarrafa fata da magungunan gargajiya da harkokin sarrafa tufafi da na gyara irin shuka da sauransu.
 • Da kuma samar da biscuit a amsana’antu da taimakon hukmar kula da kamfanonin Najeriya.
 • An kuma yi amfani da damar nan na shugaban kasa da ya bayar da damar kafa jami’ar sufuri a jihar Katsina da kuma na sufurin jirgin kasa a jihar Ogun.
 • An kuma samar da habaka sarrafa zagola ta yadda ake sarrafa shi ya koma gari da ake amfani da shi a abinci wanda yake bayar da kariya a lafiya wanda kamfanonin Turai suka amince da wannan zogalar da ake sarrafawa a Najeriya saboda ingancinsa. Haka kuma hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na kasa, NAFDAC ta amince da shi a matsayin abinci mai amfani.
 • A yanzu haka na gina kamfani tare da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu don samar da kamfanin magungunan kwari na takin zamani.
 • Samar da wani fasaha na noman doya da za a iya noma doya milyan 1-5 a duk shekara. Wannan fasahar zai samar da dankali da ayaba da arbaba.
 • Samarwa da kuma rarraba iri da maganunganan feshi da kariya daga fari kamar doya da cowpea da sauransu.

Wasanni

 • Kungiyar wasan kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru 17, Golden Eaglets, sun yi nasarar cin kofin duniya na FIFA a karo na biyar a shekarar 2015. Kuma nasararsu na farko a cikin shekara 30, a shekarar 1985 lokacin da shugaban aksa Muhammadu Buhari ke shugaban kasa a tsarin mulkin soja.
 • Najeriya ta samu shiga wasan nakasassu na Olympic a shekarar 2016 ta samu nasarar cin tagulla tun da aka fara wasan a shekarar 1992.
 • Kungiyar kwallon Kwando ta Najeriya ta mata, D’Tigress ta sami zama zakarar kwallon kwandon mata ta Afrika a shekarar 2017 wanda shi ne farko a tsawon shekara 12 wanda ta sami nasarar zuwa wasan kwallon Kwando na mata na duniya, kuma na farko tun a shekarar 2006.
 • A shekarar 2018, ta samu nasararta na farko a wasa wanda ta samu nasarar zuwa wasan gab da na kusa da na karshe, wacce ta kammala wasan a na takwas, kuma ta fi kowacce kungiya a Afrika kokari.
 • A shekarar 2019 kungiyar kwallon kwandon mata ta Najeriya ta kare kambunta na zakara da take a shekarar 2017.
 • A shekarar 2020, D’ Tigeress ta kasance kungiya daya tilo da ta samu shiga wasan Olympic ta bazara 2020.
 • Kungiyar kwallon kafa na matan Najeriya, Super Falcon ta yi nasarar lashe kofin mata na Afrika a shekarar 2016 bda 2018.
 • A shekarar 2018 an gudanar da wasannin kallon kowa na kasa na farko tun a shekarar 2012.
 • A shekarar 2018, Najeriya ta karbi bakunci babban taron FIFA na duniya, daya daga cikin 12 da aka yia
 • A shekarar 2019, kungiyar super Falcon ta haye matakin rukuni a wasan kwallon kafan mata na duniya karo na farko a cikin shekara ashirin.
 • A shekarar 2019, Najeriya ta samu nasarar tagulla a wasan tsere na duniya a cikin shekara shida.

 

Tallafawa ‘yan fina-finai

 • Babban bankin Najeriya,CBN ya samar da shirin tallafawa masana’antun fina finai da kudade tare da hadin gwiwar kwamitin bankuna domin inganta matasa a harkar fina-finai da wakoki tare da fasahar sadarwa na zamani.
 • A shekarar 2017 gwamnatin tarayya ta sanya kamfanonin fina-finai jerin cikin wadanda za a yi masu saukin biyan haraji domin kara inganata bangaren
 • Shugaban kasa ya mikawa babban zauren wasan kwaikwayo na kasa da ke Lagos ga babban bankin Najeriya da kwamitin bankuna don sake inganta harkokin yawan shakawata da na finafinai da na wakoki da kuma bangarorin fassahar sadarwa.
 • A shekarar 2017 an zabi Najeriya a matsayin mataimakiyar shugaban kungiyar yawan shakatawa na majalisar dinkin duniya.

Sabon fasalin yankin Niger Delta

Gwamnatin shugaba Buhari ta samar da sabon fasali ga yankin Niger Delta domin cika alkawuran da gwamnati ta yi wa yanki tare da samo mafita ga al’ummar yankin domin ganin su ma suna amfana da arzikin man fetur dion da Allah ya horewa yankin.

Wannan sabon fasali ya samar da abubuwa muhimmai guda 16 da aka gabatarwa shugaba Buhari a watan Nuwamba, shekara ta 2016. Sakamakon da aka samu a wannan sabon fasalin sun hada da:

 • Samar da jami’ar nazarin albarkatun ruwa da ke Okerenkoko jihar Delrta. An amince da samar da jami’ar a watan Janairu shekara ta 2018. Wanda hukuma kula da jami’o’I na kasa ta amince da fara gudanar da karatu a zangon karatu na shekarar 2017/2018, a ranar 12 ga watan Afirilu 2018.
 • Shugaba buhari ya amince da bai wa jami’ar tallafin Naira bilyan 5
 • Tsaftace Ogoni: an ware dalan Amurka milyan 170 domin tsaftace wannan yanki na Ogoni a cikin yarjejeniyar da aka yin a Escrow a watan Afrilu 2018. An soma wanann tsaftacewar ne a watan Jnairu 2019 tare da mika yanki na farko ga kamfanonin da za su yi aikin.
 • An kuma amince da hukumomi masu zaman kansu su kafa matatun mai masu zaman kansu a yanki na Niger Delta wanda yake kunshe da jihohi 9 a ciki. Wanda a yanzu nhaka na kammala guda uku sauran ana kan gina su.

Yaki da cin hanci da rashawa

Sabon tsarin fallasa:

 • Sabon tsarin fallasa na masu aikata rashawa da ma’aikatar kudi ta kirkiro a watan Disamba 2016 ya tara bilyoyin kudi daga wadanda bas a biyan haraji da kuma masu satar kudin gwamnati ( a farkon shekaru biyu da fara shirin an sami Naira biyan 7.8 da dalar Amurka milyan 378 da kuma Euro 27,800 daga barayin gwamnati ta hanayar fallasa.
 • An samar da kariya ga masu fallasaa a wani kuduri na shekarar 2019.
 • Hukumar EFCC ta kwato bilyan 794 a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 da kuma dauruwan gidaje da kaddarori.
 • Hukumar ICPC ma a karkashin shirin ta kwato sama da Naira bilyan 41 a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2019.
 • A shekarar 2019 kawai hukumar ta amshe filaye da gine-gine da ababaen hawa da kudin ya kai Naira bilyan 32.
 • Hukumar ICPC ta gudanar da bincike a cikin kudin da ake warewa na mazabu inda a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018 an sami Naira bilyan 2 da aka karkatar da su.

Karin sanya idanu a hukumomin gwamnati

Gwamnatin Buhari ta yi kokarin magance matsalolin da ake samu wajen kudaden shiga na gwamnati daga hukumomin gwamnati. A tsakanin shekarun 2010 zuwa 2016 hukumar JAMB ta Naira milyan 51. Sai gas hi hukumar ta tara Naira bilyan 20 tun daga 2017 ga gwamnatin tarayya.

Kwamitin cigaba da bincike na shugaban kasa

An kafa wannan kwamitin ne domin bincika dukkanin ma’akatu da hukumomin gwamnati tare da duba yadda ake biyan albashi. A karkashin wannan kwamitin an gano ma’akatan bogi dubu 54 wanda aka cire su, hakan yana tara wa gwamnati Naira bilyan 200 a duk shekara.

Fadada shirin asusun bai daya(TSA)

 • A ranar 7 ga watan Agusta 2015, shugaban kasa Buhari ya umurci dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su rufe asusun ajiyarsu, su kuma aikawa da dukkanin abubuwan da ke ciki zuwa baban bankin Najeriya kafain ranar 15 ga watan Satumba 2015.
 • An kaddamar da asusun bai daya a shekarar 2012 amma bai karbu ba sai da gwamnatin shugaba Buhari ta zo a watan Agusta 2015 ta kaddamar ta amfani da karfin iko. A watan May 2018 kashi 92 na ma’aikatun gwamnati sun koma tsarin asusun ajiya na bai daya.
 • Babban dalilin samar da wannan asusun ajiya na bai-daya shi ne a samu a tattara kudaden shiga na gwamnati zuwa wuri daya wanda yin haka zai takaita tare da rage almubazaaranci da kudadaen gwamnati, wanda kudaden zai rika zuwa kai tsaye a lalitar babban bankin Najeriya. A sabo da wannan shirin an rufe asusun ajiya na gwamnatu sama da dubu 17 wanda hakan kuma ya rage kasha kudaden gwamnati bilyan 4 a duk wata.
 • Wannan asusun ajiyar na bai-daya ya kawo alfanu kamar haka:
 • Ya samar da gaskiya da bindiddigi a dukkanin kudaden da gwamnati take hada-hadarsu
 • Ya toshe dukkannin wasu hanyoyi satar kudaden gwamnatin Najeriya da ake yi.
 • Ana tabbatar da cewa ana amfani da kudaden gwamnati a wuraren da suka dace
 • Ya samar da tsari a ayyukan da ake gudanarwa a kasa
 • An samu damar zuba jari mai amfani
 • Ma’aikatar kudfi ta cigaba da gudanar da wannan tsari na asusun bai-daya don tabbatar dacewa kudaden da ake samu suna shiga lalitar gwamnatin tarayya a ko yaushe.

Fadada shirin IPPIS

Duk da samun tagoci danuna hammayya a wanann shirin na IPPIS, gwamnatin shuga Buhari ta fadada shirin zuwa rundunar sojoji da kuma jam’o’o’in gwamnatin tarayya da sauran makarantun tarayya.

 

Samar da amfani da BBN a shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma

 • La’akari da yadda abubuwa suke gwamnatin tarayya ta shigar da shirin nan na samar da lambar BBN a dukkanin wani shiri na jinkai da gwamnatin take yi da tsarin fensho domin samun saukin gudanar da bincike. A karakshin wannan shirin na IPPIS gwamnati ta gano ma’aikatan bogi dubu 54 da suke cikin wadanda suke amsar albashi.
 • Gwamnatin tarayya tana amfani da lambar BBN don biyan wadaanda za su amfana da aikin dafa abinci da masu aron kudin noma da shirin N-Power don ganin cewa wadanda suka cancanta ne kawai za su amfana.

18

Samar Da Abubuwan Da Ke Taimakawa Wajen Gano Ayyukan Da Ake Yi

Ma’aikatar kudi ta tarayya ta samar da abubuwan da ke taimakawa wajen gano ayyukan da ake yi a shekarar 2016. Da wannan tsari, a karon farko gwamnatin tarayya na iya gano ayyukan da ta bayar cikin gaggawa.

Haka kuma, an kirkiri rijista na bai daya a cikin ma’aikatar domin shigar da dukkan kudaden ma’aikatar a cikin asusun gwamnatin tarayya. Wannan kokari yana daga cikin bukatocin da rahoton gyara ma’aikatun gwamnati na kasa da kasa wanda ta ma’aikatan kudin ta aiwatar da shi.

Canza Tsohon Tsarin Tsabar Kudi Zuwa Saban Tsari Wanda Ya Dace Da Zamani    

Tsarin kudin da ya dace, yana samar da gaskiya cikin shugabancin na sha’anin kudade da samar da bayanai masu inganci a kan gwamnati da kimanta harkokin kudade, domin jagorantar hukumomin kudade. Alal misali sauya tsohon tsarin kudade zuwa sabon tsari wanda ya dace, zai bayar da damar gano basussukan da ke bin ‘yan kwangila da ‘yan kasuwan mai da masu fitar da kayayyaki da kamfanoni masu rarraba wutar lantarki da dai sauran su.

Bude Damar Samun Hadin Gwiwa Da Gwamnati

A cikin watan Maris ta shekarar 2016, shugaban kasa Buhari ya hadarci taron yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kasa wanda gwamnatin Ingila ta shirya. A wannan taro, ya roki a saka Nijeriya cikin wannan shiri na hadin gwiwa domin ‘yan kasa su amfana da kyakkyawan gwamnati.

A cikin watan Yulin shekarar 2016, Nijeriya ta samu shiga cikin kasashen 70 na hadin gwiwa. Bayan haka, Nijeriya ta samu shiga cikin kwanitin gudanarwa na kasa da kasa, wanda ya bayar da damar gudanar da sharin bunkasa kasa na shekarar 2017 zuwa shekarar 2019, manufar dai yin amfani da arzikin kasa wajen inganta rayuwar mutanen Nijeriya.

A cikin shekarar 2018, an zabi kasar Nijeriya da ta garoranci hadin gwiwar gwamnatotin kasa da kasa tare da kashashen Argentina da France da kuma Romania. Dukkan wadannan kasashe guda hudu su na cikin mambobin kwamitin gudanarwa na hadin gwiwar kasa da kasa, inda za su ci gaba da shugabantar kwamitin wanda suka fara a ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 2018.

Kirkiran Albarkatun Da Gwamnati Take Da Shi Da Rage Yawan Kashe Kudade

An kirkiri wani sashin na musamman a watan Nuwamba a shekarar 2015, wanda zai rage kashe kudaden gwamnati da tabbatar da yadda ake kashe kudaden gwamnati.

Sashen yana kulawa da ma’aikatun gwamnati ta yadda suke kashe kudaden da ba su dace ba da kulawa wajen kashe kudade ta hanyar da ta dace.

Gyara Bangaren Shari’a

Shugaban kasa Buhari ya samar da kwamitin da ke bi wa shugaban kasa shawara a kan cin hanci da rashawar a cikin watan Ogustan shekarar 2015, domin cika ajandar gwamnati wajen yaki da cin hanci da rashawa da bai wa gwamnatin da ke kan mulki shawara a kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma aiwatar da gyara da sashin shari’a ke bukata. Yana daya daga cikin kwamitin na farko da shugaban kasa ya kafa bayan da aka rantsar da shi.

Kwamitin yana da ikon gudanar da ayyukanta ta hanyar saban dokar yin adalci ga manyen laifuka wanda aka samar a shekarar 2015.

Kwamitin yana gudanar da ayyuka kamar haka:

 • Horar da alkalai na tarayya da jihohi yadda ya kamata.
 • Taimaka wa hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da shawarwari ta yadda za su iya gano kadarorin da ke zargin na damfara ne da kuma gurfanar da wadanda ake zargi. A cikin ayyukansu har da sake duba dokoki kamar irin su dokokin safarar kudaden ba bisa ka’ida ba na shekarar 2004 karkashin hukumar EFCC wanda aka kafa a shekarar 2004 da hukumar ICPC wanda aka kafa a shekarar 2000, domin bayyana karfin ikon da hukumomi masu yaki da cinhanci  A Nijeriya suke da shi. Wannan kwamitin yana da matukar mahimmanci gudanar da ayyukan hukumomi masu yaki da cin hanci da rashawa.
 • Shirya taron kara wa juna sani na hukumomi da ke tsare kadarori da kuma amincewa da samar da kwamitin kulawa da kadarori. Kwamitin shugaban kasa na dawowa da kadarorin gwamnati wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yake jagoranta wanda ya samar da asusun bai daya na dawo da dukkan kudaden gwamnati wanda aka barnatar.
 • Su samar da ka’idojin na hannu wanda za su taimaka wa hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa wajen gudanar da ayyukansu. Wannan ya hada da hanyoyin gano laifukan cin hanci da rashawa ta hannu da gabatar da hujjoji na hannu da ka’idojin gurfanar da muyagun laifuka da jagojan dawo da kadarorin gwamnatin wanda aka sace da tsare-tsaren dawo wa da kundayen kadarori da bayyana laifukan cin hanci da rashawa na hannu da dai sauran su.
 • Da samar da kudirin kafa kotuna na musamma ga muyagun laifuka
 • Da fadakarwa a kan manufofin gwamnati.

Yarjejeniya Na Majalisar Gida Da Kuma Na Kasa Da Kasa 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin taimako a kan abubuwan da suka shafi laifuka, inda ya zama doka a shekarar 2019, bayan tafka mahawarar da majalisar kasa ta gudanar. Kudirin ya bayyana bincikawa da dawo da kayayyakin da aka sace tare da gurfanar da wadanda ake zargin sun aikata laifi a duk inda suke a fadin Duniya.

Nijeriya ta rattaba hannu a yarjejeniyar kasa da kasa da kasashe da dama wajen bunkasa dangantaka a hadin kai na zuba jari da bincikewa da kuma dawo da kadarorin gwamnati da aka sace

Gyara Gidajen Yari

An samu nasarar kammala gyara gidajen yarin Nijeriya a shekarar 2019, wanda suka kwashe tsawan shekara 50 ba a gyara su ba, wanda aka canza wa gidajen yarin Nijeriya suna zuwa gidan gyara halayya.

Kaddamar da sabon bayanai a kan tsarin gidajen yari. An kammala ginin gidan yarin Kuje sannan aka kaddamar da shi a watan Yulin shekarar 2017, da samar da bayanai gudanarwa wanda shi ne na farko a duk wani gidan yarin da ke Nijeriya da samar da kayayyaki na zamani kamar su kwamfutoci da samar da yanar gizo da dai sauran su. Gyara gidajen gyara halayya guda 86 a jihohi 16 da ke cikin kasar nan.

Bayan gyara dokokin yin adalci ga laifuka, a shekarar 2020, shugaban kasa Buhari ya yi wa ‘yan gidan yari guda 2,600 afuwa a dukkan gidan yarin da ke Nijeriya wanda ya rage yawan masauna gidan yarin da kashi 3.5 a Nijeriya. A cikin wadanda suka amfana da wannan afuwa su ne ‘yan shekaru 60 ko sama da haka wadanda suke fama da rashin lafiya wanda zai iya sa su mutu tare da bayar da umurnin kammala shara’o’i guda 50,000 wadanda ba a kammala ba a baya.

Tsaro

An bai wa hukumomin tsaro mahimmanci da ke fadin kasar nan, wadanda suke gudanar da ayyukan tsaro a yankin Arewa na tsakinya da na iyakokin kasar nan da sauran jami’an tsaro masu gudanar da ayyukan su a ko’ina. Gwamnatin Buhari ta bai wa jami’an tsaro mahimmanci wajen dakile matsalolin da suke fuskanta tun a shekarar 1999.

An kara samar wa jami’an tsaro bindigogi da harsasai, gwamnatin kasa da kasa sun gudanar da yarjejeniyar da gwamnatin kasar Amurka da China da Russia da Pakintan da dai sauran su, domin tallafa wa wajen gudanar tsaro a cikin kasar na. A cikin watan Afrilun shekarar 2020, zango nafarko na bataliya 17 suka isa kasar China, domin koyo dubarun yaki da kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojojin saman Nijeriya suna bukatar jirajen yaki guda 22, tun da shugaba Buhari ya hau karagan mulki a shekarar 2015, ya fara samau da guda 16 tare da yin odar 12 daga kasar Amurka wanda za a fara aiki da su a shekarar 2021. Haka kuma an kara inganta ayyukan rundunar sojojin saman Nijeriya fiye da na baya.

Rundunar sojojin ruwan Nijeriya ta samu gagaruwar canji tun  daga lokacin da shugaba Buhari ya hau kan mulki, inda suka sami sababbain kayayyakin aiki na zamani tun daga kan makamai da jirajen ruwa masu kai farmaki har guda 25 da kuma samun jiragen ruwa masu saukan angulu.

Rundunar sojojin ruwan Nijeriya ta sami ofishoshi guda 12 a bakin teku, domin dakile mayagun ayyuka nab akin teku.

A tsakanin shekarar 2015 zuwa watan Maris na shekarar 2020, rundunar sojojin Nijeriya da kakile muyagun ayyukan bakin teku guda 34, sannan suna iya gudanar da ayyukansu har na tsawon awannin 22,000 a cikin ruwa.

Rundunonin sojojin ruwa guda biyu wadanda ake kiran su da suna Tseren teku da Calm water sun dakile farmaki guda 51 a shekarar 2016, inda farmaki guda biyu aka samu nasara har zuwa watan Maris na shekarar 2020.

Rundunar sojojin ruwan Nijeriya ta samu nasarar kaddamar da gwajin kwaje bakin tekun Nijeriya wanda kasa da kasa ta amince da shi.

Rundunar sojojin ruwan Nijeriya ta samu damar bude asibiti a garin Kalaba da ke cikin Jihar Kuros Ribas a shekarar 2018, haka kuma a shekarar 2019, rundunar sojojin ruwan Nijeriya ta samu barikin a garin Banda cikin Lokoja da ke Jihar Koji.

Shugaban kasa Buhari ya sake farfado da ma’aikatar harkokin ‘yan sanda a shekarar 2019, domin kulawa da tsaro na cikin gida Nijeriya.

Shugaba Buhari ya amince da daukan sababbin ‘yan sanda har guda 10,000 a duk shekara.

Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kudurin dokar samar da kudaden ‘yan sanda a shekarar 2019, wanda wannan yana da mahimmanci ga rundunar ‘yan sandar Nijeriya.

Rundunar ‘yan sandar Nijeriya ta samu nasarar kaddamar da sabon ginin cibiyar da ke garin Abuja a shekarar 2019.

Shugaba Buhari ya kara wa sojoji da kuma ‘yan sandar Nijeriya albashi.

An samar da rundunar ta musamman a watan Maris na shekarar 2018, wanda za su gudanar da ayyuka a jihohin Benuwe da Taraba da kuma Nasarawa. Rundunar ta samu nasarar dakile ‘yan bindiga da ‘yan kungiyar asiri da masu garkuwa da mutane wanda ya kare fargici da ake samu a tsakanin shekarar 2017 da shekarar 2018.

Haka kuma an samar da rundunar ‘yan sanda da ke kulawa da bakin ruwa a watan Agusta ta shekarar 2019, wanda take gudanar da ayyukan tsaro a bakin tekun Nijeriya tare da sauran hukumomin tsaro da ke kwace kayayyakin aka yi safararsu daga kasashen ketare wanda suka hada da abinci da motoci da man fetur da taki da makamai.

Arewa Maso Gabas          

An samar da rundunoni na musamman masu yaki da Boko Haram kamar irin su Multi-National Joint Task Force (MNJTF).

Kungiyar kwallon kafa ta El-Kanemi Warriors sun kowa buga wasa a Maiduguri a watan Afrilun shekarar 2016, bayan shekara biyu da aka mayar da su Jihar Katsina saboda ayyukan masu tayar da kayan baya.

Sarkin Askira da Uba sun samu nasarar komawa gida a watan Maris na shekarar 2016, bayan shekara biyu da mayakwan Boko Haram suka sa su gudun hijira.

Makarantun gwamnati na sakandare sun koma a Jihar Borno a ranar Litinin 26 ga watan Satunbar shekarar 2016, bayan shekara biyu da rufewa.

An bude hanyar Maiduguri zuwa Gubio da kuma Maiduguri zuwa Monguno a watan Disambar shekarar 2016, bayan an rufe na tsawan shekara uku.

An samu nasarar mamaye shalkwatan ‘yan Boko Haram a dagin Sambisa a watan Disambar shekarar 2016. Bayan da rundunar sojojin Nijeriya suna kai wani farkami a ranar 26 zuwa 31 ga watan Maris na shekarar 2017.

Shugaban kiristoci a Jihar Borno ya gudanar da bikin Esta a cikin tsaro a shekarar 2017 tun bayan shekarar 2009.

Kamfanin Arik Air ya ci gaba da aiki a garin Maiduduri a watan Maris na shekarar 2017, bayan da ya yi shekara uku baya gudanar da aiki.

Rundunar sojojin Nijeriya sun bude hanyar Maiduguri zuwa Bama-Banki a watan Maris na shekarar 2018, wanda aka rufe na tsawan shekaru hudu sakamakon ayyukan Boko Haram.

Sama da miliyoyin ‘yan gudun hijira suka koma garuruwansu a yankin Arewa maso gabas tun shekarar 2015 ba sa cikin garuruwansu.

Dabban mutanen da Boko Haram suka sace an samu nasarar kwato su, wadanda suka hada da matan makarantar Chibok wanda aka sace a watan Afrilun shekarar 2014 da kuma na Dapch wanda aka sace a watan Fabrairun shekarar 2018.

Yankin Arewa Ta Tsakiya Da Arewa Ta Yamma

 • A watan Mayu 2018 hedikwatan tsaro ta kaddamar da shirin nan na ‘Operation Whirl Stroke’ hadin gwiwa ne tsakanin jam’an sojojin sama da na kasa da na ruwa da na ‘yansanda da jami’ab cibil defense da jami’an tsaron farin kaya ta DSS domin kawar da ayyukan ‘yan ta’adda da kuma ‘yanbindiga a yankin jihohin Benue da Nasarawa da Taraba. Wannan jami’an tsaro sun yi nasara wajen kawar da ayyukan ta’addanci a yankin.
 • Sake shiryawa ayyukan jami’an tsaro kan ayyukan ta’addanci da yin garkuwa da mutane da sauran ayyuka na miyagun laifuka a yankin Arewa maso yamma wanda hakan ya sanya aka kafa rundunar Operation Hadarin Daji da hedikwatan tsaro ta samar a watan Mayu 2019.
 • An kafa rundunar tsaro na THUNDER STRIKE a shekarar 2019 domin yaki da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga a bban hanyar Abuja zuwa Kaduna da kauyukan da suke hanyar.
 • Rundunar sojojin sama sun kafa 21 KRW Benue da 22 KRW a jihar Nasarawa da 23 KRW a jihar Katsina da kuma KRG 207 a jihar Zamfar don kawar da ta’addanci.
 • Haka kuma rundunar sojoiun sama ta kafa FOB a jihohin Kaduna da Katsina
 • Rundunar sojojin kasa suk kafa FOB a Kanfanin Doka da Birnin Gwari na jihar Kaduna
 • An horar da daruruwan sojojin sama da na kasa wajen kawar da ta’addanci.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: