Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa a 2027.
Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya ruwaito tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa, jam’iyyar NNPP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasa, jihohi, da sauran mukamai a fadin kasar nan a shekarar 2027.
- Gwamnonin Arewa Sun Sha Sabuwar Damara A Kan Matsalolin Yankin
- Buratai Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hajiya Dada Musa Yar’Adua
Sanata Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, ya yi magana ne a yayin kaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP a Katsina ranar Asabar.
Ya je Katsina ne domin ziyarar ta’aziyya ga iyalan ‘Yar’aduwa bisa rasuwar Hajiya Dada – Mahaifiya ga marigayi, tshohon shugaban Kasa, Alhaji Umar Musa Yar’Adua
A cewarsa, jam’iyyar na kan hanyar samun nasara a zaben 2027 mai zuwa