Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adi har zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2026, ta ɗauki matakan biyan buƙatun ma’aikata, tana mai gargaɗin cewa za ta iya ɗaukar matakin ƙasa baki ɗaya idan tattaunawar da ake yi ta gaza samar da mafita. Wannan na zuwa ne bayan wani taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.
Muƙaddashin Babban Sakataren NLC, Benson Upah, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis. Ya ce taron da aka gudanar a Ma’aikatar Ƙwadago ya tsaya cak, saboda a cewarsa, wakilan gwamnati sun zo ba tare da cikakken shiri da ikon yanke shawara kan muhimman batutuwan da ake tattaunawa a kansu ba.
Upah ya ce ba a cimma wata yarjejeniya ta zahiri ba, kuma buƙatun da ke gaban ɓangarorin biyu suna nan dai ba a warware su ba. Ya buƙaci rassan NLC na jihohi, da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da ƙungiyoyin farar hula da ke goyon bayanta su kasance cikin shiri tare da fara shirye-shiryen yiwuwar ɗaukar mataki a faɗin ƙasa. Sai dai ya jaddada cewa ƙungiyar na fatan gwamnati za ta biya buƙatunta ta hanyar tattaunawa.
Ya bayyana cewa an ɗage taron zuwa ranar 27 ga Oktoba ne bisa buƙatar Ministan Ƙwadago, domin bai wa gwamnati damar tattara ministocin da abin ya shafa da shugabannin hukumomin gwamnati domin ci gaba da tattaunawa. Daga cikin buƙatun NLC akwai rage farashin fetur zuwa matakin da yake a shekarar 2024, sake tattauna kan mafi ƙarancin albashi na ƙasa da kuma aiwatar da yarjejeniyar rage haraji ga ma’aikata.
Sauran buƙatun sun haɗa da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da Ƙungiyoyin Ƙwadago na Ma’aikatan Lafiya (JOHESU), da kuma buƙatun Majalisar Tattaunawa kan Albashin Ma’aikatan Gwamnati (JPSNC), ciki har da alawus-alawus na musamman, da ƙarin tallafin albashi da alawus na hatsari.
NLC ta ce za ta ci gaba da bin hanyoyin tattaunawa, amma ba za ta amince da jinkiri marar iyaka ba. Ta kuma bayyana cewa shugabancinta zai yanke shawarar mataki na gaba idan taron ranar Talata bai samar da gagarumin ci gaba ba.














