Hukumomin Ƙasar Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa a kan wasu ƴan ƙasar Bangladesh biyu, Nazrul Islam Abdul Basir da Siti Akhtar, bayan samunsu da laifin aikata baɗala da lalata a cikin wani masallaci a birni mai tsarki na Makkah. Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana cewa an aiwatar da hukuncin ne a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2026.
Bayanai sun nuna cewa jami’an tsaron ƙasar sun cafke mutanen biyu ne a daidai lokacin da lamarin ya auku, inda aka gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotun da ta dace. Kotun ta same su da babban laifi tare da yanke musu hukuncin kisa a ƙarƙashin tsarin Ta’azir (hukuncin da alƙali ke yankewa a shari’ar Musulunci domin ladabtarwa), sakamakon girman laifin da kuma keta alfarmar wuri mai tsarki da suka yi.
Hukuncin kisan ya zama tabbatacce ne bayan da kotun ɗaukaka ƙara da manyan hukumomin shari’a na ƙasar suka amince da shi, sannan aka fitar da umarnin masarauta (royal order) domin zartar da kisan bisa tanadin Shari’ar Musulunci. An zartar da hukuncin a ranar Laraba bayan kammala dukkan matakan shari’a da doka ta tanada.
Ma’aikatar Cikin Gidan ta jaddada aniyar Gwamnatin Saudiyya ta tsare tsaro, da wanzar da adalci, da kuma aiwatar da dokokin Shari’a kan duk wanda ya keta alfarmar masallatai ko mutuncin al’umma.
Hukumar ta kuma fitar da gargaɗi mai ƙarfi cewa ba za ta lamunci kowane irin laifi da zai taɓa tsarkin wuraren ibada ba, kuma duk wanda aka samu zai fuskanci mummunan hukunci ba tare da ɗaga ƙafa ba.













