Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta fitar da sunayen mambobin kwamitin ba da shawara kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan jihar gabanin zaɓen 2027.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci kwamitin, yayin da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, zai zama mataimakin shugaban kwamitin.
Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, da Kwamandan Hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Sauran sun haɗa da Sheikh Ali Dan Abba da Sheikh Nazifi Bichi.
Haka kuma, tsofaffin gwamnonin jihar Abdullahi Umar Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Kabiru Gaya, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin da sauran manyan ’yan siyasa na cikin kwamitin.
Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Umar Haruna Doguwa ne, ya fitar da jerin sunayen, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana.














