ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

by Abubakar Sulaiman
4 hours ago
Obasanjo

Olujonwo Obasanjo, ɗa ga tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya sanar da shiga ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’, wadda ke fafutukar ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da mulki bayan shekarar 2027. Olujonwo ya bayyana matakinsa ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abuja a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 2026, inda shugabancin ƙungiyar ta Tinubu Movement for Sustainable Governance Foundation (TMS) ya karɓe shi hannu biyu-biyu.

Da yake jawabi a wurin taron, Olujonwo ya bayyana cewa shawarar tasa ta samo asali ne daga ƙwarewarsa a fagen siyasa, sanin tarihin sauye-sauyen tsare-tsare a Nijeriya, da kuma imanin da yake da shi kan cewa ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin gwamnati ba tare da katsewa ba shi ne zai kawo ci gaban ƙasa. Ya jaddada cewa ba baƙo ba ne a jam’iyya mai mulki, domin yana cikin APC tun kafuwarta a shekarar 2014 a lokacin da mahaifinsa ya karɓi baƙuncin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu.

Olujonwo ya koka da yadda rashin isar da bayanai masu inganci ke bai wa masu adawa damar yaɗa labaran ƙarya da gurɓata kyakkyawan aikin da gwamnatin Tinubu ke yi. Ya nuna cewa a ƙarƙashin wannan gwamnati, an kawo ƙarshen yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU), an kaddamar da shirin bayar da rancen karatu ga ɗalibai (Student Loan), kuma ana ta gine-gine aiyukan more rauwa da jan hankalin masu zuba jari. Ya ce aikin TMS shi ne fito da waɗannan manufofi a fili da kuma bayyana fa’idarsu ga talakawan ƙasar maimakon dogaro da taken siyasa kawai.

ADVERTISEMENT

A nasa jawabin, Babban Kodinetan Ƙungiyar ta TMS kuma Darakta Janar na Hukumar NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, ya bayyana jin daɗinsa kan shigowar Olujonwo, yana mai cewa ya fito ne daga dangin da suka kafa tubalin sauye-sauyen tattalin arziƙi na zamani a Nijeriya, musamman a fannin sadarwa da tsarin bankuna. Kashifu Abdullahi ya yi gargaɗin cewa yawan sauya tsare-tsare na lalata kwarin gwiwar masu zuba jari, yana mai nuni da cewa tsare-tsaren Tinubu na ƙara ƙarfafa darajar Naira, da kasuwar hannayen jari, da kuma matatar mai ta Dangote.

Shi ma a nasa ɓangaren, Darakta Janar na TMS, Marcel Ngogbehei wanda tsohon jigo ne a tafiyar Obidient ya bayyana shigowar Olujonwo a matsayin wani gagarumin ci gaba ga tafiyar. Ya jaddada cewa an kafa ƙungiyar ne domin zaburar da al’umma su fahimci ainihin manufofin gwamnati, da daƙile kuskuren fahimta, da kuma tabbatar da cewa tsare-tsaren Shugaba Tinubu sun ɗore bayan babban zaɓen 2027.

LABARAI MASU NASABA

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027

Obasanjo
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
  • Abubakar Sulaiman
    Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC
  • Abubakar Sulaiman
    Aikin Titin Jirgin Ƙasa Na Kaduna Zuwa Kano Ya Kai Kashi 90%
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola

MASU ALAKA

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo
Siyasa

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

October 22, 2026
Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027
Siyasa

Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027

October 22, 2026
Atiku Ba Shi Da Gogewar Da Zai Farfaɗo Da Tattalin Arziƙin Nijeriya – Sakataren APC Na Ƙasa
Siyasa

Atiku Ba Shi Da Gogewar Da Zai Farfaɗo Da Tattalin Arziƙin Nijeriya – Sakataren APC Na Ƙasa

October 22, 2026
Next Post
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne - Sheikh Disina

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.