Ina kira ga daukacin ‘yan kasar nan a kowane sashi suke su yi rajistar zabe saboda kalubalen da ke tattare da zabe mai zuwa. Ga dalilaina guda uku na yin wanna kira.
Ambaliya
Sakamakon zaben fid da gwani na ‘yan takarar shugaban kasa ya kawo ambaliyar masu rajistar jefa kuri’a, musamman a yankunan Inyamurai da Yarbawa.
Dafifin mutanen ba karami ba ne, domin ya sa har hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kara na’urorin rajista a jihohi biyar a yankunan Inyamurai da Jihar Legas da kuma Jihar Kano. 5-1-1. Me wannan lissafin ya nuna maka? Kuma me ya jawo wannan dafifi?
Ina ga ba zai rasa nasaba da kokarin da kowane sashi yake yi ba don ya taimaka wa nasa dan takarar da kuri’u masu yawa, don idan kowanne zai samu daukacin masu jefa kuri’a a sashinsa, ba shakka likkafarsa za ta ja gaba.
A nan, ‘yan arewa suna da matsalar ko-oho (complacency) ganin cewa suna da yawa. Ina ga wannan babban kusukure ne. Jefa kuri’a a yau ya zama wajibi ga duk wanda yake son ya ga an samu ci gaba a kan abin da ya dame shi. Yau muna cikin tasku na rashin zaman lafiya.
Ya kamata a ce mun fi kowa damuwa da waye zai zama shugaban kasa, saboda shi ne zai shugabanci hukumomin tsaro gaba daya. Idan wani zai yi amfani da su ya taimake mu, wani zai iya amfani da su ya cutar da mu.
In mun yi watsi da zabe mai zuwa, yana yiyuwa abubuwa su kara tabarbarewa har inda fitinar ba ta kai ba yau ta kai a gobe, ko a bullo da wasu sababbin fitinu. Su ma sauran sassan kasar suna da abubuwan da ke damunsu kuma a kan haka za su jefa kuri’a. To me zai sa ba za mu himmatu ba kamar yadda suke nuna himma a kwanakin nan?
Tuwon Gobe
Na yarda akwai mutane da yawa da rashin kyan mulkin Buhari ya kashe wa gwiwa. Ga mai hankali, wannan shi ne ma zai sa a kara himma, a gwada wani watakila a yi dace, domin ana zaton wuta a makera a same ta a masaka. Ala ayyi halin, mu ‘yan kasa mu yi namu. Mu zaba. Idan wadanda muka zaba suka ci amanarmu ko suka gaza, sai mu bar su da Allah. Rashin dadin tuwon yau ba shi zai hana mu cin na gobe ba.
Ingancin Zabe
Bugu da kari, yau kuri’a tana da muhimmanci ba kamar a baya ba, don an ci karfin magudi a lokacin zabe. Wannan ci gaba ya samu ne don rajistar masu jefa kuri’a da aka samar tun zamanin marigayi Yar’adua (Allah ya masa rahama), da amfani da fasahohin zamani na tantance masu jefa kuri’a, da aikawa da sakamako daga mazabu kai-tsaye zuwa rumbun bayanai na INEC, da kuma uwa-uba dokoki daban-dabam da ke cikin dokokin zabe da aka kafa tun 2011.
Yau idan mutum ya jefa kuri’a akwai tabbaci mai rinjaye cewa za a kirga ta a yawan kuri’un dan takarar da ya jefawa. Me ya fi haka dadi? Ba a gama seta komi da komi ba, amma dai an ci karfin magudi. Wanda aka tafka a shekarun baya ba za a sake iya yin sa ba a yanzu. Don haka wadanda da suke cewa kuri’arsu ba ta da amfani, ya kamata su bar wannan turbar, su fara yin zabe.
Sakiyar Da Ba Ruwa
Don wadannan dalilai, ina kira ga kowa ya tsaya kan wadanda yake da iko a kansu ko wadanda suke jin maganarsa ya tabbatar da kowannensu ya yi rajista. Kuma idan lokacin zabe ya zo, kowa ya jefa kuri’arsa ga wanda ya fi zaton zai fi alheri da kawo ci gaba a kasa.