Shafin da ke zakulo maku sanannun mutane, wanda suka hadar da Jaruman fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood, masu ba da umarni da shiryawa, har ma da mawaka manya da kanana kana da fitattun da ke zagawa a ko ina.
A yau ma shafin ya zakulo maku wani shahararren mai shirya fina-finan Hausa cikin masana’antar Kannywood, kuma me ba da umarni kuma me hada hoto a cikin masana’antar, wato HUSSAIN M. IBRAHIM wanda aka fi sani da HUSSAIN BACCI.
Jarumin ya yi bayani game da yadda ya tsinci kansa cikin masana’antar Kannywood, tare da bawa sauran abokan aikinsa shawarwari da ma sauran bayanai. Wakilinmu YAKUBU FURIDUSA ya zanta da jarumin inda ya fara da cewa;
Da farko za mu so ka gayawa masu karatu cikakken sunan da sunan da aka fi saninka da shi
Sanana Hussein M. Ibrahim (Hussein Bacci)
Me ya ja hankalin Hussain shiga wannan Masana’anta?
To na shigo fim ne ta hanyar dan uwana wato Aminu Bacci (Edita) a matsayin zan koyi hada hoto (Editing) Alhamdulillah na koyi Editing din, wanda daga baya na juya na koma Producer/Director wanda a kalla zuwa yanzu na yi ‘Producing din fim dina sama da goma.
Bayan shirya fim da ba da umarni da kake yi shin ka taba fitowa a matsayin jarumi?
Eh! ina yi.
Fina-finan da ka yi za su kai kamar guda nawa?
Na yi fim a kalla za su kai goma wanda ba na wani bane nawa ne
Me yasa mutane suke maku wani irin kallo idan an ce kai dan fim ne ko ma’aikacin fim, akwai wani abu da ake fada kan ta waye ana yi wa sabbin Jarumai, shin ka taba yi kai ma idan aka zo wajanka aiki, ko aka kawo maka kwangilar aiki?
To ni dai wannan abin kan ta waye ban san shi ba. Sanann kuma duk wata sana’a da mutum yake yana samun kalubale, amma ta fim daban take, wacce babu yadda za ka yi da abin da mutane za su ce a kan ka don ka shiga fim ko kana harkar fim.
Akwai fim dinka na ‘Mayafin Sharri’ daya tsaya ana cikin ci gaba da nemansa, shin matsala ka samu da ‘yan wasan ko kai ne ka yi wasa da damarka?
A’a ‘MAYAFIN SHARRI’ ana nan ana yinsa har yanzu.
Wannne fim ka fi so a cikin duk fina-finanka?
Suna da yawa.
Kasancewarka na Furodusa kuma Edito yaya kake iya hada gudu da susar mazaunai idan aikin ya hade maka da aikin da kake na zama?
To ai kowanne lokacinsa nake bashi shiyasa ba ya yi min wahala.
Shin kana da aure?
Ana shirin yi dai nan da wasu lokuta masu zuwa.
Idan wata jarumar ta yi yunkurin aurerka, shin za ka iya aurar jaruma?
Me zai hana matukar tana sona, kuma za ta cika duk wani sharadi wanda aure ya tanadar.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da sana’arka ta fim da kuma editin, wanda har kake nadamar shigarka cikin masana’antar?
Gaskiya babu wani fim da na taba yin nadamar yinsa.
Ko kana da ubangida a harkar fim?
Aminu Mu’azu Ibrahim (Aminu Bacci).
Wacce shawara za ka bawa ‘yan uwa abokan aikinka na editin da furodusin?
Shawarata daya ce su tsaya akan gaskiyar su ga duk wanda ya kawo musu aiki ka da su dubi cewa wannan Madaukaki ne, wanan kuma kawai yana yin fim ne. Sanan ka da wani editor ya dauka wani madaukaki ko furodusas suna yawan murunci to babu wani murunci sai don su ci moriyarka wanda da zarar an samu wasu wanda suka fika ko kuma ma suke dai-dai da kai to za su koma wajensa ne sakamakon kana bunsu bashi.
Wacce shawara za ka bawa furodusas akan yadda za su gudanar da aikinsu?
To shawara daya ce zuwa biyu mutun ya dauki ma’aunin duk wani aikin fim da zai yi akanbcewa me zan yi wanda zai yi wa Allah dadi da wanda ba zai yi wa Allah dadi ba.
Muna godiya ka huta lafiya.
Nima na gode.