ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 20, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Radda Ya Ƙaddamar Da Shirin Tsaron Abinci Da Tallafawa Matasa A Katsina

by Sulaiman
51 minutes ago

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da wani shirin inganta tsaron abinci na dala miliyan 1, tare da sanar da tallafin kuɗi har Naira miliyan 1 ga matasa masu harkar noma da mata domin ƙarfafa samar da abinci da inganta rayuwar al’umma.

Shirin mai taken “Kare Tsaron Abinci Daga Ambaliyar Ruwa Da Fari”, ƙungiyar Mercy Corps Nigeria ce za ta aiwatar tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Ci gaban Jihar Katsina da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki.

Gwamna Radda ya ce shirin na tsawon watanni 12 zai fara ne a ƙananan hukumomin Bindawa, Bakori da Kafur, domin taimaka wa manoma wajen fuskantar matsalolin sauyin yanayi.

ADVERTISEMENT

Ya ce za a gyara rijiyoyin ruwa masu amfani da hasken rana guda 12, inganta gonaki 150, farfaɗo da filayen da suka lalace, gyara rumbunan ajiyar abinci 150, tare da raba buhunan adana hatsi guda 500.

Shirin zai kuma tallafa wa noman da ya dace da sauyin yanayi, samar da wasu hanyoyin samun kuɗin shiga ga mata kusan 300, da kuma ayyukan samun kuɗi kai tsaye ga mutane 180.

LABARAI MASU NASABA

Pate Ya Jinjina Wa Sauye-sauye Da Inganta Harkokin Lafiya A Katsina

Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?

A wani ɓangare, Radda ya sanar da tallafin fara sana’a na Naira miliyan 1 ga kowane ɗaya daga cikin matasa 361 da suka kammala zangon biyu na shirin koyar da noma na DRATESS-Songhai.

Ya ce kowanne daga cikin waɗanda suka amfana zai fara da N500,000, yayin da za a sakin sauran kuɗin a matakai bisa yadda suka kafa sana’o’insu da kuma yadda suke gudanar da su.

Gwamnan ya kuma ce za a faɗaɗa cibiyar Makera Songhai domin ta riƙa ɗaukar mutane har 1,000, yana kira ga waɗanda suka kammala horon da su mayar da ilimin zuwa sana’o’i tare da samar da ayyukan yi.

Haka kuma, Radda ya duba wata motar gyara ta tafi-da-gidanka da aka saya domin gyara da kula da taraktocin jihar guda 400 a yankunan manoma.

Majalisar Zartarwar Jihar ta kuma amince da shirin tallafa wa mata 49,640 a unguwanni 361 da ƙananan hukumomi 34, tare da amincewa da aikin sake gina hanyar Bindawa–Dallaje–Doro–Giremawa–Duwan zuwa mahaɗar Duwan.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Pate Ya Jinjina Wa Sauye-sauye Da Inganta Harkokin Lafiya A Katsina
  • Sulaiman
    An Bude Bikin Fina-Finai Na Kasa Da Kasa Na Hanyar Siliki Karo Na 13 A Xi’an
  • Sulaiman
    Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?
  • Sulaiman
    An Bude Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Asiya Karo Na 20 A Nagoya Na Japan

MASU ALAKA

Pate Ya Jinjina Wa Sauye-sauye Da Inganta Harkokin Lafiya A Katsina
Labarai

Pate Ya Jinjina Wa Sauye-sauye Da Inganta Harkokin Lafiya A Katsina

September 20, 2026
Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?
Wasanni

Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?

September 20, 2026
Trump Ya Hana CNN Da Wasu Kafofin Yaɗa Labarai Shiga Fadar White House
Kasashen Ketare

Trump Ya Hana CNN Da Wasu Kafofin Yaɗa Labarai Shiga Fadar White House

September 19, 2026

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Radda Ya Ƙaddamar Da Shirin Tsaron Abinci Da Tallafawa Matasa A Katsina

September 20, 2026
Pate Ya Jinjina Wa Sauye-sauye Da Inganta Harkokin Lafiya A Katsina

Pate Ya Jinjina Wa Sauye-sauye Da Inganta Harkokin Lafiya A Katsina

September 20, 2026
An Bude Bikin Fina-Finai Na Kasa Da Kasa Na Hanyar Siliki Karo Na 13 A Xi’an

An Bude Bikin Fina-Finai Na Kasa Da Kasa Na Hanyar Siliki Karo Na 13 A Xi’an

September 20, 2026
Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?

Ko Kano Pillars Za Su Iya Taka Wa Doma United Burki A Yau?

September 20, 2026
An Bude Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Asiya Karo Na 20 A Nagoya Na Japan

An Bude Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Asiya Karo Na 20 A Nagoya Na Japan

September 20, 2026
Trump Ya Hana CNN Da Wasu Kafofin Yaɗa Labarai Shiga Fadar White House

Trump Ya Hana CNN Da Wasu Kafofin Yaɗa Labarai Shiga Fadar White House

September 19, 2026
Adadin Tafiye-Tafiyen Da Jiragen Kasa Masu Jigilar Fasinjoji Suka Yi A Sin Ya Kai Matsayin Koli A Watanni 8 Na Bana

Adadin Tafiye-Tafiyen Da Jiragen Kasa Masu Jigilar Fasinjoji Suka Yi A Sin Ya Kai Matsayin Koli A Watanni 8 Na Bana

September 19, 2026
Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Bauchi Ta Yi Allah-wadai Da Kama Masu Kaɗa Ƙuri’a

Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Bauchi Ta Yi Allah-wadai Da Kama Masu Kaɗa Ƙuri’a

September 19, 2026
Kungiyar ’Yan Kasuwar Kaduna Ta Rantsar Da Sabon Shugaban Riƙo

Kungiyar ’Yan Kasuwar Kaduna Ta Rantsar Da Sabon Shugaban Riƙo

September 19, 2026
Sin Na Fatan Inganta Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya Na MDD

Sin Na Fatan Inganta Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya Na MDD

September 19, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.