An bude bikin fina-finai na kasa da kasa na hanyar siliki karo na 13 a birnin Xi’an na lardin Shaanxi da yammacin jiya 19 ga wata, karkashin taken “hanyar siliki na hade mabambantan wurare a duniya, fina-finai na haskaka a Chang’an”.
Wannan bikin na kunshe da zaben lambar yabo ta “hanyar siliki ta zinari”, hadin gwiwa ta kasa da kasa da masana’antu, kirkire-kirkire na fasaha da sabbin hanyoyin kasuwanci, nuna fina-finai da amfanin al’umma da al’adu.
Bugu da kari, wannan bikin ya kafa tsarin hadin gwiwa mai zurfi na kasa mai masaukin baki a karon farko, inda aka gayyaci Masar ta zama kasa mai masaukin baki, don gudanar da bikin nuna fina-finai da tattaunawa kan abin ya shafa, aka kuma sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin bikin fina-finai na kasa da kasa na hanyar siliki da bikin fina-finai na kasa da kasa na Alkahira, matakin da ya gina sabon dandali na hadin gwiwar fina-finai tsakanin Sin da Masar, da kuma kara wa bikin fina-finai na kasa da kasa na hanyar siliki sabon kuzari da karfi.
An gudanar da bikin fina-finai na kasa da kasa na hanyar siliki karo na 13 ne da hadin gwiwar Babban rukunin gidan radiyo da talabijin na kasar Sin CMG da gwamnatin lardin Shaanxi da gwamnatin lardin Fujian. (Amina Xu)













