Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, kan zuba jari da gwamnatin jihar ke yi wajen inganta harkokin lafiya.
Pate ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya kaddamar da sabon gyaran Babban Asibitin Charanchi, tare da ƙaddamar da baburan daukar marasa lafiya 238 masu kafa uku da kuma motocin agajin gaggawa 18 masu ɗauke da kayan tallafawa rayuwa.
Ministan ya kuma duba wasu ayyukan da ake gudanarwa a Babban Asibitin Kwararru na General Amadi Rimi da ke Katsina, ciki har da cibiyar killace marasa lafiya, cibiyar dialysis da cibiyar daukar hoton cikin jiki, inda ya bayyana gamsuwa da ayyukan.
Pate ya ce yawan mutanen da suka yi rajista da tsarin inshorar lafiya a Katsina ya karu daga kusan 350,000 a shekarar 2023 zuwa kusan 600,000 a shekarar 2026. Ya kuma ce sama da mutane 184,000 ne aka yi wa rajista a cikin kananan hukumomi da unguwanni 361 ta hanyar Asusun Kula da Kiwon Lafiya a Makakin Farko (Basic Health Care Provision Fund).
A nasa bangaren, Gwamna Radda ya ce motocin daukar marasa lafiyar za su taimaka wajen rage jinkirin kai marasa lafiya asibiti, musamman a yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa.
Ya ce baburan masu kafa ukun 238 da aka kaddamar su ne kashi na farko cikin 361 da aka tsara rabawa ga unguwanni 361 na jihar.
Radda ya kuma bayyana cewa an gyara sama da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Farko 280, yayin da ake kafa wasu cibiyoyin lafiya manya guda shida a fadin jihar.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin tasa ta samar da inshorar lafiya kyauta ga fursunoni 20,000, mutane masu nakasa 20,000 da jami’an tsaron al’umma 50,000, tare da daukar ma’aikatan lafiya sama da 3,800 aiki a cibiyoyin lafiya na matakai daban-daban.














