An bude gasar wasannin motsa jiki ta Asiya karo na 20 a birnin Nagoya na lardin Aichi na Japan da yammacin jiya 19 ga watan nan da muke ciki.
Da misalin karfe 6 na maraice bisa agogon kasar Japan, aka fara bikin bude gasar a filin wasan motsa jiki na Mizuho Park, inda ’yan wasa daga kasashe da yankuna 45 suka shiga daya bayan daya.
Tawagar Sin a wannan karo ta kunshi ’yan wasa 815, kuma za su shiga fafatawa a manyan wasanni 38 da kananan wasanni 369. (Amina Xu)
ADVERTISEMENT














