Ana wa matasa kirari daban-daban a cikin al’umma, tun daga lokacin yarinta da ake ce musu “yara manyan gobe” har zuwa cewa “matasa su ne kashin bayan ci gaban al’umma”, domin nuna irin muhimmancin da suke da shi ga raya ci gaban kasa da kuma al’umma baki daya.A kasar Sin, tun yara suna kanana ake renonsu game da kishin gina kasa.
Ana sanar da su muhimman abubuwa da suka shafi aiki tukuru, da tambarin kasa kamar tuta da taurarin cikinta da ma’anarsu, da muhimman wurare masu nasaba da gina ci gaban kasar ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa har kuma zuwa lokacin da za su kai shekarun balaga da za su fara shiga cikin harkokin raya kasa ka’in-da-na’in.Irin wannan tarbiyya mai ban sha’awa, ana koyar da ita ta hanyoyi da dama, tun daga cikin iyali, zuwa makarantu da kuma kafofin watsa labarai.
Akwai wani shiri na gidan rediyo da aka fara gabatar da shi tun a ranar 4 ga Satumbar 1956 mai suna Xiaolaba, wato “karamin kakaki” da ya kasance shirin rediyo na farko a Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da aka kebe musamman domin yaran da ba su kai shekarun shiga makaranta ba.
Shirin wanda ya gawurta har ya zama babban shirin da ake watsawa a rediyo, da talabijin, da shafukan sada zumunta da shirye-shiryen yada labarai na cikin makarantu, yana bayar da labarai ne masu dadi ga yara dake kunshe da hikimomi da sauran al’amura da suka shafi gina tunanin yara a turba mai kyau.
A lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake taya murnar cika shekaru 70 da fara gabatar da wannan shiri, ya jaddada kira ga kwararru a fannin tarbiyyantar da yara su kara azama wajen renon matasa su zamo masu kwarewa don su ci gaba da raya tafarkin gurguzu.
Kazalika, a wani jawabi da na ci karo da shi kwanan nan na shugaba Xi, na ga yadda ya ba da muhimmanci sosai a kan kira ga matasa su rika daidaita burikansu na rayuwa da na ci gaban kasa, inda hakan ke nuna muhimmancin gudunmawar matasan ga raya kasa. Kazalika, a wani bangare na kokarin da ake yi a kan renon matasa a turbar gina ci gaban kasa da hidimta wa al’umma, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kan tura matasa da suka yi rajistar zama mambobinta zuwa yankunan karkara domin gudanar da ayyukan hidimta wa jama’a ko da kuwa daga birane suka fito. Haka nan, ana tura kwararrun matasa daga fannonin ilimin aikin gona zuwa kauyuka don taimaka wa manoma da dabarun aiki na zamani.
Tabbas, irin wannan reno da kasar Sin ke wa matasa a kan kyakkyawar turba, ya sa matasan kasar nuna jajircewa wajen ba da gudunmawa ga ci gaban kasar ta fuskoki da dama, walau a karkashin kungiyoyinsu ko dandalolinsu.
Kuma ya dace musamman ga kasashe masu tasowa, su ba da karfi ga renon matasansu a kyakkyawar turba domin taimaka wa burikansu na gina kakkarfan ci gaban kasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














