Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce ko kadan kasar Sin ba ta taba janyewa wata kasa tsani ba, maimakon hakan, har kullum tana samar da tsani ne ga dukkanin kasashe, ta yadda za su taka zuwa kaiwa ga manyan matsayi.
Mao Ning, wadda ta bayyana hakan a Larabar nan, ta ce a ko da yaushe kasar Sin na neman hanyoyi ne na cimma moriyar bai daya, da samun ci gaba tare, kana ta zame wa kasashe masu tasowa kawa abar dogaro, tana kuma samar da gudunmawar bunkasa kasashe masu tasowa daga ci gaban da take samu.
Mao Ning, ta kara da cewa karkashin hadin gwiwar aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya mai matukar inganci, Sin tana kara taimakawa kasashe abokan huldarta da damar cike gibin ababen more rayuwa.
Kazalika, ta hanyar samarwa kasashe masu tasowa kayayyakin ayyukan masana’antu masu rahusa, da fasahohin sarrafa hajoji, da horon kwarewa da sanin makamar aiki, Sin ta taimaka wajen rage tsadar ayyukan raya masana’antun kasashen.
Bugu da kari, bisa manufar Sin ta kawar da daukacin harajin kwastam, da manufar shigo da hajoji cikin kasar Sin, an samar da karin riba da damarmakin kasuwa, wadanda suka baiwa kasashe masu tasowa ikon kara dunkulewa cikin tsarin hada-hadar hajoji na duniya, da kyautata juriyar yanayin ci gaba. (Saminu Alhassan)














