Albarkacin ranar malaman makaranta ta kasar Sin wadda ake bikinta a duk ranar 10 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika gaisuwa ga malamai, da jami’an fannin ilimi dake aiki a daukacin sassan kasar Sin.
A sakon na taya murnar wannan rana, shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kira ga daukacin malaman makaranta dake kasar da su kara azamar inganta kwarewarsu, da sanin makamar aiki, kana su samar da sabbin rukunin matasa da za su iya sauke nauyin burin cimma nasarar farfado da kasa. (Saminu Alhassn)
ADVERTISEMENT














