Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta roƙi al’ummar Kudu maso Gabas da su sake zaɓar mijinta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Da take magana a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ranar Laraba, Remi ta ce tana son ganin Nijeriya ta samu ci gaba domin ita da mijinta su more ƙasar a lokacin tsufansu.
Ta yi wannan kira ne yayin wani shiri na tallafa wa mata, inda mata 2,500 a Jihar Imo suka samu kayan tallafi domin gudanar da sana’o’insu.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce shirin, wanda ake gudanar da shi a faɗin ƙasar, zai tallafa wa mata 18,500.
Za a ba su kayan aiki kamar janareta, injin niƙa, gas da murhu domin bunƙasa sana’o’insu.
Bayan Gwamna Hope Uzodimma ya bai wa mata 2,000 tallafi a jihar, Remi Tinubu ta sanar da ƙarin tallafin Naira 100,000 ga kowace daga cikin mata 2,500 da suka amfana da shirin.
Gwamna Uzodimma ya yaba da shirin tare da bayyana cewa al’ummar Imo za su goyi bayan Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.














