A kwanan nan kusan duk kafofin watsa labarai na cikin gida da kuma sauran shafukan sada zumunta masu yawa a sassan duniya, sun cika da labarai da hotuna game da wani salo da ake yayi mai lakabin “China Cool”, da ke nufin “Kasar Sin mai dadin zuwa” ko kuma na ce “kasar Sin mai ni’ima”.
Abin da ya sabbaba salon shi ne dadin da ake ji a wurare masu ni’ima saboda yanayin garjen rana na lokacin zafi da ake ciki yanzu haka. Baki daga sassa daban-daban na duniya musamman ma daga yankunan kasashen Turai da ke fama da tsananin zafi, suna kara tuttudowa zuwa kasar Sin domin more wannan salo da ake yayi. Wannan salo na kokarin tsere wa tsananin zafi ya bai wa wasu gundumomi damar samun tagomashi. Misali, a gundumar Zherong da ke lardin Fujian, wacce saboda yanayinta na na’ima ba a cika bukatar amfani da na’urar sanyaya daki ba a lokacin zafi, adadin masaukai da ake kamawa a otel-otel ya ninka da kusan sau 10 a mizanin shekara-shekara.
Haka nan gundumar Yanshan da ke lardin Jiangxi, wacce take kewayen wurin shakatawa na kasa na tsaunin Wuyi da ke da gandun daji mai yawa, ta samu karin baki masu kawo ziyara da ninki uku. Ita ma gundumar Changli ta lardin Hebei ta shiga jerin wuraren yawon shakatawa na matakin gunduma guda 20 da suka fi samun bunkasar harkokin yawon bude. Kazalika, cinikin kama masaukai a dakunan otel-otel a gundumomin Fusong da Antu da ke yankin wurin shakatawa na tsaunuka a lardin Jilin ya karu da kusan ninki biyu.
Irin wannan ci gaba da ake samu a gundumomi na da alaka kai-tsaye da yadda kasar Sin take kokarin habaka yankunanta na karkara a bisa yanayin da suke ciki. Ba wai a canja su kwata-kwata daga asalinsu su koma kamar birane ba, amma a yi kyakkyawan tunani kan yadda za a bunkasa ci gabansu bisa hakikanin asalinsu. Daya daga cikin hikimomin jagoranci da jam’iyyar JKS mai mulkin kasar Sin ke amfani da su shi ne, fadada tunani game da yadda za a ci gajiyar yanayin da wuri yake ciki.
Irin wannan ne ya haifar da bunkasa yankuna masu yawan zubar dusar kankara zuwa cin gajiyar yanayinsu ta hanyar yawon bude ido da wasannin motsa jiki kamar yadda ake iya gani a birnin Harbin na lardin Heilongjiang. Haka nan, aka bunkasa arzikin gora a gundumar Anji ta birnin Huzhou da birnin Lishui, dukkansu da ke kardin Zhejiang, da sauran misalai da dama.
Idan aka dubi wannan, ko shakka babu za a iya fahimtar cewa, a bisa turbar ci gaba da kasar Sin ke kai wacce ake kara bunkasa ta zuwa zamanantarwa, aka samar da kyakkyawan yanayi ga muhallan wuraren da baki ke zuwa don more salon da ake yayi na “China Cool” domin samun sa’ida a lokacin nan na zafi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














