Kungiyar Dattawan Arewa ta ACF reshen Jihar Kano ta gindaya sharudda ga dukkan ‘yan takarar gwamna da ke jam’iyyu daban-daban wadanda suke son gadar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a 2023.
Shugaban kungiyar na Jihar Kano, Dakta Farouk Umar shi ya bayyana wa ‘yan jarida hakan a ranar Lahadin da ta gabata. Ya ce manufar yin hakan shi ne, dattaunawa da ‘yan takarar domin jin abubuwan da za su yi wa jihar idan aka zabe su.
Ya ce, “A cikin sharuddan da muka ginda ya musa a lokacin da suka samu nasara ban da yin katsalandan a cikin harkokin kudaden kananan hukumomin jihar da muke da su.
“Sannan na biyu, mun bukaci su da su tabbatar da cewa a cikin jami’ansu tun daga kan kwamishinoni da babban sakatarori da shugabannin ma’aikatu kar su kai ‘ya’yansu karatu waje, su tabbatar sun yi karatu a makarantun gwamnati saboda su san matsalolin da suka turnike harkokin iliminmu.
“Haka kuma mun bukaci su tabbatar da cewa babu rikice-rikice a yakin neman zabensu, domin mu samu kamfen mai cike da zaman lafiya da kuma zabe, sannan sun rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da kin yin amfani da ‘yan daba wajen kamfen dinsu.”
Bisa zirgin da ake yi kan harkokin siyasar Kano wajen kai hare-hare da abokan hamayya da yin amfani da ‘yan daba, ta sa ita kungiyar ACF rashen jihar ta gindaya wadannan sharudde a tsakanin ‘yan takara, domin samun damar tattaunawa da su wajen samun zaman lafiya da lumana a cikin harkokin siyasar jihar.
Masu ruwa da tsaki a cikin harkokin siyasa su ne suka gana da kungiyar ACF tare da bayyana musu cewa su ja kannuan ‘yan siyasar jihar wajen samun zaman lafiya yayin gudanar da harkokin siyasa a cikin jihar.
Da yake jawabi bayan ganawar sirri da dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Aminu Abdussalam, daya daga cikin shugabannin kungiyar, Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana cewa akwai fargaba game da abubuwan da suke faruwa a siyasar Jihar Kano.
Ya ce, “A matsayinmu na dattawa dole mu nuna wa wadannan ‘yan takara abubuwan da muke so da kuma wadanda ba ma so masu kawo tashin hankali da tarwaza zaman lafiya, ba za mu taba hade hannu ba mu bari ana gudanar da gubataccen siyasa a Jihar Kano.”
Fagge ya kara da cewa sun tattauna da ‘yan takarar gwamna domin kokarin samar da zaman lafiya da hanyar dakile rikice-rikice.