Ƙungiyar Tinubu Support Group (TSG) ta yi gargaɗin cewa sake dawo da tallafin man fetur na iya mayar da tattalin arziƙin Nijeriya baya da shekaru 20.
Ƙungiyar ta zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da yin alƙawuran siyasa kan tallafin man fetur gabanin zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa, Darakta-Janar na ƙungiyar, Umar Tanko Yakasai, ya ce dawo da tallafin zai iya ƙara wa gwamnatin nauyin kuɗi tare da rage ƙwarin gwiwar masu zuba jari.
Ya ce Nijeriya ta riga ta fuskanci mawuyacin lokacin cire tallafin, don haka ya kamata a mayar da hankali wajen ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar maimakon komawa tsohon tsarin.
Yakasai ya kuma yi tambaya kan matsayar Atiku game da tallafin man fetur, yana mai cewa a baya tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya goyi bayan cire tallafin.
Ya bukƙci ’yan Nijeriya su duba tare da tantance alƙawuran ’yan siyasa da suka shafi farashin man fetur da tallafi gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta kuma ambaci wasu alƙaluman tattalin arziƙi, inda ta ce tattalin arziƙin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin 100 a zangon na biyu na shekarar 2026, idan aka kwatanta da kashi 3.89 cikin 100 a zangon farko na shekarar.














