’Yan bindiga sun kashe mata uku tare da jikkata wani mutum yayin da suka kai hari wani wajen haƙar ma’adinai a garin Rakum, ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato a ranar Litinin.
Rahotanni sun ce maharan sun isa wajen da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda suka buɗe wa ma’aikatan wajen wuta kafin su tsere.
Mai magana da yawun Ƙungiyar Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da harin tare da kira ga jami’an tsaro da su kamo waɗanda suka aikata laifin.
Wani mazaunin yankin, John Silas, shi ma ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa lamarin ya ƙara haifar da fargaba tsakanin mazauna yankin da ma’aikatan wajen.
Harin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-hare a wasu sassan Jihar Filato ciki har da Mangu, Barkin Ladi, Riyom da Bokkos.
Hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.














