Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ce buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta neman amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin karɓar sabon bashin ƙasashen waje ta tabbatar da gargadin da ya yi a baya kan shirin gwamnati na ƙarin bashi.
Tinubu ya nemi amincewa da rancen dala biliyan 20.52 da kuma Yuro biliyan 1.045 domin gudanar da ayyuka da shirye-shirye a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da samar da ababen more rayuwa, noma, lafiya, ilimi da tsaro.
Atiku, wanda yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya ce a ranar 12 ga Oktoba ya yi gargaɗin cewa gwamnati na shirin karɓar bashin da ya kai dala biliyan 20, musamman dangane da aikin Babbar Hanyar Gabar Teku ta Legas zuwa Kalaba.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya nuna damuwa kan rashin bayyana cikakken bayani game da ayyukan da za a kashe kuɗin a kansu, kuɗin kowane aiki, wuraren da za a gudanar da su da kuma kamfanonin da za su aiwatar da su.
Ya kuma yi tambaya kan yiwuwar amfani da wasu ayyukan gwamnati wajen karkatar da kuɗin bashin zuwa ga ’yan siyasa da ’yan kwangila masu kusanci da gwamnati. Sai dai wannan zargi ne da Atiku ya yi, ba hujjar da aka tabbatar ba.
Atiku ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta dakatar da amincewa da bashin har sai gwamnati ta bayyana cikakken bayanin ayyukan da za a gudanar, yarjejeniyoyin kwangila, kuɗaɗen da ake buƙata, sharuɗɗan rancen da kuma yadda za a biya bashin.
Ya kuma yi gargaɗin cewa ya kamata a tabbatar da duk wani sabon bashi ya bi ƙa’idojin kundin tsarin mulki da dokokin ƙasar.
A nasa ɓangaren, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa rancen zai taimaka wajen cike gibin samar da ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar ’yan Nijeriya. Ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na ƙasar.
A ranar Talata, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce za a miƙa buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Basussukan Cikin Gida da na Ƙasashen Waje domin nazari, tare da yiwuwar haɗa kai da kwamitocin kasafin kuɗi da kuɗi.














